
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis Babbar Kotun Jihar Adamawa ta yanke wa wasu mutane uku hukuncin kisa kan garkuwa da wasu limaman Cocin Catholika guda biyu a watan Fabarairun 2025.
Da yake gabatar da hukunci, Mai Shari’a Christopher Mapeo ya ce ya samu mutane ukun ne da hannu a makircin aikata laifin garkuwa, makircin aikata fashi da makami, fashi da makami, ɓoye wanda aka yi garkuwa da shi da tattaunawar karɓar kuɗin fansa domin sako Fada Matthew Dutsemi da Fada Abraham Sauman. Akan haka ne alƙalin ya yanke wa Teledo Demiel, Namomai Medan da Mikaila Yusuf hukuncin kisa kan garkuwa, fashi da makami da wasu laifuka.
Wannan shi ne hukuncin kisa na bakwai da Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) ta samar a wannan shekarar. A ranar 20 ga Mayu 2026 ne wata Babbar Kotu a Jihar Ekiti ta yanke wa wasu mutum biyu, Ibrahim Abubakar da Abdullahi Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun su da laifin garkuwa.
Bayan sati biyu a ranar 3 ga Yuni, 2026 ne Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yanke wa mutum huɗu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa hannu a kisan kiyashin Yunin 2022 na wasu ‘yan cocin St. Francis Catholic Church da ke Owo a Jihar Ondo. Mutanen sune Idris Abdulmalik Omeiza, Alqasim Idris, Jamiu Abdulmalik da Abdulkareem Idris.
Sannan, a ranar 15 ga Yunin ne dai Babbar Kotun Jihar Katsina ta yanke wa wata mata mai suna Hauwa’u Mukhtar hukuncin kisa bayan samun ta da hannu a safarar makamai ga ‘yan ta’adda. A washe-gari a ranar 16 ga Yunin ne wata Babbar Kotun Jihar Kogi ta yanke wa wani Jibrin Halilu hukuncin rataya kan garkuwa da halaka moƙocinsa a garin Obajana da ke jihar.
Kazalika, bayan mako guda ne Babbar Kotun Jihar Sakkwato ta yanke hukuncin kisa akan Muhammed Yusuf Sallau, Jabbi Ahlaji Yale da Kabiru Muhammed ta hanyar rataya bayan samun su da laifukan ta’addanci da safarar makamai. Sannan, a Satumbar 2026 ne kotun ta yanke wa Ibrahim Usman da aka sani da Ɗan Iyali hukuncin kisa kan hannu a halaka mutum uku da ya yi garkuwa da su a jihar.
