Ƙudirin kafa ‘yan sandan jihohi ya samu amincewar majalisun dokokin jihohi 24

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sashen Doka na Constitution (Sixth Alteration) na 2026 wanda ya bayar da damar samar da tsarin ‘yan sanda biyu a Nijeriya, ya samu amincewar majalisun dokokin jihohi guda 24, wanda ke nuna ya cika ƙa’idar samun amincewar kaso biyu cikin uku na jihohi 36 na faɗin Nijeriya da ake buƙata kafin aiwatarwa.

Kwamitin Shugaban Ƙasa da ke aiki kan Ƙudirin Ƙasa kan kafa ‘Yan sandan Jihohi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, wanda ke ɗauke da sanya hannun Shugabansa kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Kwamitin ya kuma yaba wa majalisun dokokin jihohin bisa ɗaukar muhimmin matakin gyaran dokar domin samar da tsarin a Nijeriya, yana mai bayyana hakan a matsayin “gyaran muhimmin al’amarin ƙasa”. Ya kuma yaba wa Majalisar Dokokin Ƙasa kan amince wa yi wa ƙudirin karatu na uku tare da tabbatar da shi.

A cewar sanarwar, za a maido da kwafin ƙudirin ga Majalisar Dokokin Ƙasa domin ta yi masa nazarin ƙarshe tare da isar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu don tabbatarwa, bisa aiki da hukuncin Sashe na 9 na Dokar Ƙasa.

Amincewa da wannan ƙudiri za ta bayar da damar amfani da tsarin ‘yan sanda kala biyu a Nijeriya mai suna National Policing Bill, 2026, wanda aka tsara aiwatarwa. Kazalika, kwamitin ya bayyana cewa a yanzu haka ana yin nazarin doka da ƙoƙarin tantancewa a Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya.

Sannan, za a mayar da shi ga kwamitin kafin ko a ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026 domin dubiya ta ƙarshe kana a gabatar wa Shugaban Ƙasar, inda kwamitin ya kirayi masu ruwa da tsaki da su bayar da cikakken haɗin kai wajen samun nasara yayin aiwatar da tsarin.

By Babaji

Leave a Reply