
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa (NEC) ta amince da tara aiwatar da shirin samar da sauƙin halin matsin rayuwa na tsawon wata uku da Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta gabatar domin isar da amfanin gyare-gyaren tattali da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samar, da nufin rage tsadar rayuwa da inganta hanyoyin samun rahusar farashin kayan abinci.
Wannan shiri kuma yana da nufin fifita janyo ra’ayin masu zuba jari da hanzarta kammala muhimman ayyukan ababen more rayuwa domin amfanin ‘yan Nijeriya. A cewar sanarwar da Kakakin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha ya fitar, ya ce an amince da shirin ne bayan da Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele ya gabatar wa majalisar a taron NEC karo na 161, wanda aka gudanar a ranar Alhamis ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.
Muhimman al’amura biyar da shirin ya ƙunsa sun haɗa da samar da sauƙin farashin kayan masarufi, sauƙaƙe matakan haraji, kammala muhimman ayyukan ababen more rayuwa ta yadda za a ga tasirinsu acikin al’umma, faɗaɗa damarmakin zuba jari da gudanar da ayyukan tallafa wa magidanta.
Haka kuma, NEC ta amince da samar da tsarin ƙasa na tantance halin muhimman ayyukan ababen more rayuwa a sassan ƙasar da nufin tabbatar da gaskiya da adalci da bayar da sahihin rahoto kan yadda aka sarrafa kuɗaɗen cire tallafin fetur.
Da yake gabatar da jaddawalin tattalin, Oyedele ya bayyana ƙwarin-gwiwarsa kan shirin gyare-gyaren harkar tattali da gwamnatin Tinubu ke yi da kuma matakan da ake ɗauke na farfaɗowa daga halin matsin tattali.
Ya bayyana cewa, babbar manufar shirin shi ne rage matakan hauhawar farashi da riba (Interest) zuwa ƙaramin mataki, yana mai cewa gaɓa ta gaba ita ce aiwatarwa a matakin ƙasa da cibiyoyin jihohi, yana mai cewa hakan na da nufin samar da sauƙi a halin zamantakewar al’umma ta yau da kullum.
