
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027 ya buƙaci a hanzarta wallafa jaddawalin rajistar masu zaɓe, yana mai gargaɗin rashin yin hakan a yanar gizo daga ɓangaren Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ka iya zama barazana ga sahihancin zaɓukan 2027.
Atiku, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ta hannun Daraktan Dabarun Sadarwa na kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC (ADC-PCC), Phrank Shaibu, ya ce ‘yan Nijeriya suna da ‘yancin sanya ido kan rajistar, ƙalubalantar wasu ababe da ba su gamsu da su ba aciki da kuma gyara dukkan wasu kurakurai gabanin gudanar da zaɓen.
“INEC ta sanar da cewa sama da masu rajistar zaɓe miliyan 103 ne ake da su. ‘Yan Nijeriya sun je shafinta na yanar gizo domin duba sunayensu, sai suka samu babu komai a shafin, …a nuna wa ‘yan Nijeriya rajistar,” inji shi.
A kwanakin baya ne dai INEC ta sanar da cewa za ta fitar wa al’umma bayanan rajistar masu zaɓe a tsakanin ranakun 9 da 15 ga Oktoba, inda ake sa ran masu zaɓe za su yi nazari kan sahihancin rajistar, yin wasu tambayoyi, ƙalubalantar dukkan wani waje da suke ganin bai yi daidai ba da kuma ruwaito batun sunayen da ba a gani ba.
A cewar Atiku, rashin sanya jaddawalin rajistar a yanar gizon daga INEC ya saɓa wa Dokar Zaɓe ta 2026 da kuma tayar da ƙura kan sahihancin hanyoyin gudanar da zaɓe a Nijeriya. Ya kafa hujja da Sashe na 19(1) na dokar, wanda ya hukunta wallafa rajistar masu zaɓe a wuraren rajista da yanar gizo, yana mai kira ga INEC da ta wallafa su a matakan ƙananan hukumomi, yanki da kuma gunduma.
Haka kuma, ɗan takarar shugaban ƙasar ya buƙaci a warware kalamai masu cin karo da juna da aka alaƙanta su da shugaban hukumar akan lokacin wallafar, yana mai kira ga INEC da ta fitar da kwanan wata, adireshin yanar gizo da matakin samun rahotannin da aka yi zargin suna da alaƙa da wallafar intanet.
