Daga JOHN D. WADA a Lafia
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ɗauki matakai domin hana ɓarkewar cutar Ebola a jihar bayan tabbatar d lamarin a babban birnin tarayya Abuja.
Babban sakatare na ma’aikatar lafiya Dr. Ibrahim Alhassan ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata hira da jaridar Manhaja a Lafia babban birnin jihar inda yace jihar ta sake buɗe cibiyoyinta na killace marasa lafiya tare da yaɗa shawarwarin kiwon lafiyar jama’a.
Yace ma’aikatar ta shirya shawarwari na musamman da aka rarraba ga ƙwararrun jami’an kiwon lafiya da kuma jama’a baki ɗaya kan alamomin cutar, yadda ake kamuwa da ita da kuma hanyoyin kariya.
A cewarsa, jihar ta kafa wata tawaga ta musamman da babban likitan cututtuka na jihar zai jagoranta domin ci gaba da bibiyar masu mu’amala da marasa lafiya, sa ido da wayar da kai.
Ya bayyana cewa tawagar za ta haɗa kai da kafafen yaɗa labarai a wani shirin wayar da kai da kwamishinan lafiya zai ƙaddamar a wani taron manema labarai a mako mai zuwa.
“Taron manema labarai zai fara wayar da kai da faɗakarwa kan menene cutar, menene alamominta, yadda ake yaɗa ta, da kuma abin da mutane ke buƙatar yi domin kare kansu,” in ji shi.
Alhassan yace gwamnati na kuma siyan kayan kariya na mutum, PPE, tare da ajiye su a cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban, yayin da jami’an sa ido kan cututtuka a ƙananan hukumomi 13 na jihar aka tura su kuma aka sanya su cikin shirin ko-ta-kwana, musamman a manyan tashoshin mota da wuraren zirga-zirgar matafiya.
Yace ma’aikatar na kuma aiki tuƙuru wajen ƙara wayar da kan ma’aikatan lafiya, tare da umartar su da su mayar da martani cikin gaggawa ga duk wani lamari da ake zargi, su killace inda ya dace, su tattara cikakken bayani kan tarihin tafiye-tafiye da mu’amala, sannan su miƙa lamuran zuwa matakai uku na kiwon lafiya – firamare, sakandare da manyan asibitoci.
Haka kuma darakta mai kula da lafiyar jama’a Dr. Peter Attah, ya ce an tuntuɓi abokan huldar cikin gida da na ƙasa da ƙasa, ciki har da hukumar lafiya ta duniya, WHO, domin ƙarfafa shirin jihar na gaggauta mayar da martani.
Ma’aikatar tuni ta fitar da shawarar kiwon lafiyar jama’a mai kwanan wata 21 ga Oktoba, 2026 kuma darakta mai kula da lafiyar lama’a, Dr. Attah Peter Ombugadu ya sanya wa hannu, inda ta umarci dukkan cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati da masu zaman kansu da kuma jami’an sa Ido kan cututtuka na ƙananan hukumomi da su ƙara sa ido tare da gaggauta bayar da rahoton duk wani lamari da ake zargi ta hanyoyin da aka tanada ba tare da jiran tabbacin ɗakin gwaji ba.
