Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN) ta bayyana cewa filayen jiragen sama uku daga cikin 22 da take gudanarwa ne ke kula da kusan kashi 80 cikin 100 na zirga-zirgar jiragen sama a Nijeriya, lamarin da ke nuna ƙalubalen da hukumar ke fuskanta wajen raba kuɗaɗen inganta ababen more rayuwa tsakanin manyan filayen jiragen sama da sauran filayen da ke faɗin ƙasar.
Manajan Darakta kuma Babbar Jami’ar Gudanarwa ta FAAN, Olubunmi Kuku, ta bayyana filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas a matsayin mafi yawan zirga-zirgar jiragen sama a ƙasar, inda yake da kashi 68 cikin 100 na jimillar zirga-zirgar da hukumar ke kula da su.
Ta ce filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ne ke biye da shi, sai kuma filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano.
Da take jawabi a matsayin babbar mai gabatar da muhawara a bikin World Aviation Festival da aka gudanar a Lisbon, ƙasar Portugal, kan taken “Tsara Filin Jirgin Sama na Gaba: Fasaha, Haɗin Gwiwa da Mutane”, Kuku ta ce yawan zirga-zirgar fasinjoji a wasu manyan filayen jiragen sama kaɗan na buƙatar tsari mai kyau wajen zuba jari.
Ta bayyana cewa wannan tsari ya kamata ya mayar da hankali kan tsaron ayyuka, ingancin ababen more rayuwa da kyautata jin daɗin fasinjoji, ba tare da yin watsi da sauran filayen jiragen saman ƙasar ba.
“Filayen jiragen sama uku ne ke kula da kashi 80 cikin 100 na zirga-zirgar, amma har yanzu ina da wasu 19, sannan akwai wasu filayen jiragen sama biyar da nake tallafawa, waɗanda su ma nake buƙatar ba su fifiko,” inji ta.
Bayanin da shugabar FAAN ta bayar ya nuna ƙalubalen da hukumar ke fuskanta wajen rarraba kuɗaɗen zuba jari, yayin da take ƙoƙarin zamanantar da manyan filayen jiragen saman ƙasar, tare da kula da ababen more rayuwa da ingancin ayyuka a sauran filayen da take gudanarwa.
Kuku ta ce hukumar tana amfani da manyan ƙa’idoji guda uku wajen tsara, inda za ta fi maida hankali wajen zuba jari, inda tsaro yake a matsayin babban fifiko, musamman wajen gudanar da ayyukan gyaran sassan filin jirgin da jiragen sama ke tashi da sauka.
“Abu na farko shi ne ƙa’ida bayyananniya da ta mayar da hankali kan tsaro. Saboda haka, za ku ga cewa yawancin jarin da muke zubawa yana kan wasu ayyuka a sassan filin da jiragen sama ke tashi da sauka, domin waɗannan su ne muhimman wuraren da muke buƙatar tabbatar da cewa ayyukanmu na yau da kullum suna tafiya yadda ya kamata,” in ji Kuku.
Ta ƙara da cewa a cikin shekaru uku da suka gabata, FAAN ta mayar da hankali kan gyaran manyan filayen jiragen sama, musamman waɗanda ake amfani da su wajen zirga-zirgar ƙasa da ƙasa.
A cewarta, hukumar tana gudanar da ayyukan gyaran titunan da jiragen sama ke amfani da su, ciki har da sake shimfiɗa su gaba ɗaya da kuma tsawaita su a wuraren da hakan zai yiwu. Haka kuma, tana girka ingantattun fitilun hasken filin jirgin a wasu filayen.
Filayen jiragen sama shida na ƙasa da ƙasa a Nijeriya suna Legas, Abuja, Fatakwal, Kano, Enugu da Maiduguri.
Saboda kasancewarsa filin jirgin sama mafi yawan zirga-zirga a ƙasar, ana gudanar da babban aikin zamanantar da tashar fasinjoji a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas, domin inganta ayyuka, sauƙaƙa wa fasinjoji gudanar da matakan tafiya da kuma kyautata ƙwarewarsu wajen amfani da filin jirgin.
Kuku ta ce ana sake fasalta Tasha ta 1 ta filin jirgin gaba ɗaya, maimakon faɗaɗa ta, domin inganta yadda ake amfani da sararin da ake da shi da kuma sauƙaƙa zirga-zirgar fasinjoji a wuraren binciken shige da fice, kwastam da sauran matakan tantancewa.
