Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta nuna rashin amincewa da damuwar da Bankin Duniya ya bayyana kan tafiyar da kuɗaɗen shigar ƙasar wajen biyan ribar bashin da ta kai Naira tiriliyan 7.7 a farkon shekarar 2026, inda bankin ya yi gargaɗin cewa hakan na iya jefa ɗorewar bashin Nijeriya cikin barazana.
Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ce ta bayyana matsayinta cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, wadda Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele, ya wallafa a shafinsa na ɗ.
A sabon rahotonsa kan ci gaban Nijeriya, wato Nigeria Development Update, Bankin Duniya ya nuna damuwa kan yadda kuɗaɗen shiga na gwamnati ke tafiya wajen biyan bashin ƙasar a farkon shekarar 2026, inda ya ce kuɗin biyan bashin ya kai kashi 124 cikin 100 na kuɗaɗen shiga.
Sai dai Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta ce yanayin kuɗaɗen gwamnati ya inganta, domin kuɗaɗen shiga na ƙasa na ƙaruwa cikin sauri fiye da kuɗin da ake kashewa wajen biyan ribar basussuka.
Ma’aikatar ta bayyana rahotannin da ke cewa kuɗin ribar bashin ya kai kashi 124 cikin 100 na kuɗaɗen shigar Gwamnatin Tarayya a lokacin a matsayin masu yaudarar fahimta. Ta ce an samo wannan ƙididdiga ne daga bayanan kuɗaɗen shiga da ba su cika ba, sannan aka haɗa da basussukan da gwamnatin tarayya ke biya a madadin gwamnatocin jihohi. Haka kuma, ma’aikatar ta ce ƙididdigar ba ta haɗa da kuɗaɗen shiga da hukumomi da kamfanonin gwamnati suka samu amma ba su miƙa wa baitul malin gwamnati ba.
Ta ƙara da cewa, bisa tanade-tanaden dokoki, wasu haraji ba a fi karɓar su sai a rabin na biyu na shekara. Saboda haka, amfani da kuɗaɗen shiga na watanni shida na farko wajen tantance nauyin bashin shekara baki ɗaya na iya haifar da sakamakon da bai nuna ainihin yanayin kuɗaɗen gwamnati ba. Sanarwar ta ce, “Ma’aikatar Kuɗin Tarayya ta lura da wasu nazarce-nazarce da maganganun da ake yaɗawa a bainar jama’a, waɗanda suka danganta da rahoton Bankin Duniya na watan Oktoban 2026 kan ci gaban Nijeriya, suna ikirarin cewa kuɗin ribar bashin Gwamnatin Tarayya ya kai kashi 124 cikin 100 na kuɗaɗen shigarta a farkon rabin shekarar 2026. Wannan matsaya ba ta nuna cikakken hoto ba, saboda dalilai uku.”
Ma’aikatar ta bayyana cewa adadin kuɗin ribar bashin da aka yi amfani da shi ya haɗa da basussukan da Gwamnatin Tarayya ke biya a madadin sauran matakan gwamnati, ciki har da bashin ƙasashen waje da gwamnatocin jihohi suka karɓa. Ta ce kwatanta irin waɗannan basussuka da kuɗaɗen shigar gwamnatin tarayya kaɗai yana ƙara nuna nauyin bashin fiye da ainihin yadda yake, domin ingantacciyar ƙididdiga na buƙatar a kwatanta bashin da kuɗaɗen shiga na matakin gwamnati guda.
Sanarwar ta kuma ce bayanan kuɗaɗen shiga da aka yi amfani da su ba su cika ba, saboda ba su haɗa da kuɗaɗen da hukumomi da kamfanonin gwamnati suka samu da kansu amma ba su miƙa wa baitul malin gwamnati ba.
Dangane da lokacin karɓar haraji, ma’aikatar ta bayyana cewa ana samun ƙarin kuɗaɗen shiga a rabin na biyu na shekara fiye da rabin farko, saboda lokacin da doka ta tsara na biyan wasu haraji. Ta ce wannan ne ya sa rabon kuɗin biyan bashin da kuɗaɗen shiga ya kai kashi 156 cikin 100 a farkon rabin shekarar 2025, alhali a ƙarshen shekarar gaba ɗaya ya kasance ƙasa da kashi 60 cikin 100, bayan saukowa daga kashi 97 cikin 100 kafin aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki.
Ma’aikatar ta ce wannan ci gaba ya nuna tasirin sauye-sauyen da gwamnatin yanzu ta aiwatar. Ta bayyana cewa tsakanin farkon rabin shekarar 2025 da makamancin lokacin shekarar 2026, kuɗaɗen shigar Gwamnatin Tarayya sun ƙaru da kashi 72 cikin 100, daga naira tiriliyan 3.6 zuwa naira tiriliyan 6.2. A gefe guda kuma, kuɗin ribar bashin ya ƙaru da kashi 38 cikin 100 kacal, daga Naira tiriliyan 5.6 zuwa Naira tiriliyan 7.7.
A cewar ma’aikatar, hakan na nufin kuɗaɗen shiga na ƙaruwa da kusan ninki biyu na saurin da kuɗin ribar bashin ke ƙaruwa. Ta ce sakamakon haka, rabon ribar bashin da kuɗaɗen shiga ya ragu da maki 32 cikin shekara guda, daga kashi 156 zuwa kashi 124 cikin 100. Haka kuma, tazarar da ke tsakanin kuɗin shiga da ribar bashin ta ragu daga naira tiriliyan 2 zuwa naira tiriliyan 1.5.
Ma’aikatar ta jaddada cewa wannan ci gaba sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki ne, ba alamar durƙushewar kuɗaɗen gwamnati ba. Ta kuma ce ana tantance dorewar bashin ƙasa ne bisa bayanan shekara baki ɗaya, ba na watanni shida kawai ba. A cewar ma’aikatar, rahoton Bankin Duniya ɗin ya yi hasashen cewa jimillar kuɗin da Nijeriya za ta kashe wajen biyan bashinta a shekarar 2026, ciki har da babban bashin da ribarsa, zai kai kashi 46 cikin 100 na kuɗaɗen shiga.
Ma’aikatar ta bayyana wannan ƙididdiga a matsayin ma’aunin da ya dace wajen tantance halin bashin ƙasar, tare da gargaɗin cewa bai kamata a yanke hukunci daga bayanan da ba su nuna cikakken yanayin shekara ba. Ta ƙara da cewa duk bashin da Gwamnatin Tarayya ta karɓa yana cikin iyakar rancen da Majalisar Dokoki ta ƙasa ta amince da shi a ƙarƙashin Dokar Kasafin Kuɗi ta 2026 da tsarin karɓar bashi da aka amince da shi.
Sanarwar ta ce ana karɓar dukkan basussukan ne bisa cikakken bin Dokar Kula da Kuɗaɗen Gwamnati ta 2007 da Dokar Kafa Ofishin Kula da Basussukan ƙasa ta 2003. Ta kuma ce Ofishin Kula da Basussukan ƙasa (DMO) na wallafa bayanan basussukan a kai a kai.
A ƙarshe, ma’aikatar ta ce tana maraba da sahihin bincike da nazari kan harkokin kuɗaɗen gwamnati. Sai dai ta buƙaci manazarta da masu sharhi da su yi amfani da irin tsauraran matakan tantance bayanai da suke buƙatar gwamnati ta bi, ta hanyar kwatanta abubuwan da suka dace, duba ƙididdiga cikin mahallinsu da kuma neman ƙarin bayani idan akwai rashin tabbas.
