Mafarauta sun kashe ‘yan bindiga 14 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mafarauta sun sami nasarar halaka ‘yan bindiga 14 a ƙauyen Gidan Kawo a ƙaramar hukumar Bakori na Jihar Katsina.

Sanarwar ɗauke da sa hannun kwamishin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya bayyana cewa ‘yan bindiga su 26 ɗauke da manyan makamai bisa Babura 13 ƙarƙashin jagorancin Isiya Kwashan Garwa suke tafiya akan hanyar su ta zuwa dajin Laila.

Jami’an tsaro a ƙaramar hukumar suka zama cikin shiri koda ta kwana bayan samun bayanan sirri kan yunƙuri da yan bindiga suke yi na kai hare hare a wasu ƙauyuka.

Cikin dare ‘yan bindigan suka kai hari ga wata mota mallakar Jamilu LawaL wanda ke tare da wasu mutane uku da suka fito daga ƙauyen Kakumi akan hanyar su ta zuwa cikin kasuwar Illela a Jihar Sokoto.

To sai dai bayan musayar wuta mafarautar yankin Bakori suka sami nasarar hallaka ‘yan bindiga 14 wasu kuma suka gudu suna ɗauke da manyan rauni,su kuma ‘yan bindigan su kashe mutun ɗaya da ke cikin motar tare da ƙona motar amma sauran mutane uku da ke cikin motar sun sami nasarar kuɓuta ba tare da ko ƙwarzani ba,haka kuma sun kashe ɗaya daga cikin mafarauta a ɗauki da daɗin da ya gudana.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati da haɗin gwiwa na jami’an tsaro sun ƙoƙarin ganin sun maganin irin wannan hare hare a yankin.

By ukarofi

Leave a Reply