Fasfon Nijeriya ya faɗi daga matsayi na 90 zuwa na 181 a duniya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Fasfon Nijeriya ya faɗi daga matsayi na 90 a watan Yulin 2026 zuwa na 181 cikin ƙasashe 196 a sabon jadawalin Iziɓisa na fasfo na ƙasashen duniya, lamarin da ke nuna raguwar ƙasashen da ’yan Nijeriya za su iya ziyarta ba tare da neman biza tun kafin tafiya ba.

Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa, bisa bayanan da aka wallafa a shafin Iziɓisa.com, masu fasfon Nijeriya za su iya shiga ƙasashe 24 ba tare da biza ba, samun biza a lokacin da suka isa ƙasashe 16, sannan su samu biza ta intanet domin shiga ƙasashe 43.

Sabon jadawalin ya nuna gagarumin koma-baya daga matsayi na 90 da Nijeriya ta kasance a kai a watan Yulin 2026, lokacin da masu fasfon ƙasar za su iya shiga ƙasashe 44 ba tare da biza ba.

Raguwar yawan ƙasashen da za a iya shiga ba tare da biza ba daga 44 zuwa 24 na nuna bambancin da ke tsakanin jadawalan biyu da kuma raguwar ƙasashen da ’yan Nijeriya za su iya ziyarta ba tare da samun izinin biza tun kafin tafiya ba.

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta, Iziɓisa ta bayyana cewa ana tsara matsayin fasfo ne bisa yawan ƙasashen da masu shi za su iya shiga ba tare da neman biza tun kafin tafiya ba.

Jadawalin yana la’akari da hanyoyin shiga ƙasashe daban-daban, ciki har da shiga ba tare da biza ba, samun biza a lokacin isowa da kuma biza ta intanet, waɗanda ke nuna irin damar zirga-zirgar ƙasashen duniya da masu fasfo suke da ita.

ƙasar Haɗaɗɗliyar Daular Larabawa (UAE) ce ta zo ta farko a jadawalin Iziɓisa na shekarar 2026, inda fasfon ƙasar ke ba masu shi damar shiga wurare 185 cikin wurare 198 da aka tantance ta hanyar shiga ba tare da biza ba, samun biza a lokacin isowa ko kuma biza ta intanet.

Switzerland ta zo ta biyu, inda masu fasfon ƙasar za su iya shiga wurare 120 ba tare da biza ba, wurare 26 ta hanyar samun biza a lokacin isowa, sannan wurare 37 ta hanyar biza ta intanet.

Sauran ƙasashen da suka yi fice a jadawalin sun haɗa da Luɗembourg, Malta, Denmark, Spain da Finland.

Iziɓisa ta bayyana cewa bambancin da ke tsakanin fasfon ƙasashen da suka fi matsayi da waɗanda suka zo ƙasa yana nuna babban gibi wajen damar zirga-zirgar ƙasashen duniya. Jadawalin yana amfani da yawan wuraren da za a iya shiga ba tare da biza tun kafin tafiya ba a matsayin ma’aunin ’yancin zirga-zirga.

A wani jadawali na daban, rahoton Henley Passport Indeɗ na watan Yulin 2026 ya sanya Nijeriya a matsayi na 90 cikin fasfo 199 da aka tantance a duniya, inda masu fasfon ƙasar za su iya shiga wurare 44 ba tare da biza ba.

Jadawalin da Henley & Partners ta fitar ya nuna cewa Nijeriya ta faɗi matsayi ɗaya daga na 89 da ta kasance a kai a rahoton Afrilun 2026, duk da cewa adadin wuraren da za a iya shiga ba tare da biza ba bai sauya daga 44 ba.

A cewar Henley & Partners, jadawalin na shekarar 2026 ya kasance wani ɓangare na bikin cika shekaru 20 da kafuwar ƙungiyar, inda aka tantance fasfo 199 bisa wuraren tafiye-tafiye 227, ta amfani da bayanan Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (IATA).

A tsakanin ƙasashen Afirka, Afirka ta Kudu ta zo matsayi na 49 a duniya, inda masu fasfon ƙasar za su iya shiga wurare 101 ba tare da biza ba. Botswana ta biyo baya a matsayi na 61, tana da damar shiga wurare 81, yayin da Morocco ta zo ta 67 da wurare 71.

Kenya ta kasance a matsayi na 68, inda za a iya shiga wurare 70 da fasfon ƙasar ba tare da biza ba, yayin da Ghana ta zo ta 70 da damar shiga wurare 67.

Nijeriya ta kasance a matsayi ɗaya da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Turkmenistan, inda kowace ƙasa ke da damar shiga wurare 44 ba tare da biza ba, bisa jadawalin Henley.

Rahoton Iziɓisa ya nuna babban bambanci da matsayin Nijeriya a jadawalin Henley na watan Yuli. Sai dai jadawalan biyu suna amfani da hanyoyin tantancewa da kuma bayanai daban-daban, don haka bai kamata a ɗauke su a matsayin jadawali guda ɗaya da ake iya kwatantawa kai tsaye ba.

By ukarofi

Leave a Reply