Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Mataimakiyar ’yar takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar NDP mai alamar fitila, Ambasada Hajiya Sameera Bala Usman, ta ce jam’iyyarsu za ta kawo sauyi mai kyau da zai bunƙasa rayuwar al’ummar Jihar Kano.
Ambasada Sameera ta bayyana haka ne a wata hira da ta yi da ’yan jarida kan dalilin shigarta jam’iyyar NDP da kuma tsayawa takarar mataimakiyar gwamna.
Ta ce ta zaɓi NDP ne saboda jam’iyyar ta ba mata muhimmanci da dama fiye da sauran jam’iyyu.
“Jam’iyyun da muke da su yanzu, waɗanda suke kafa gwamnati, ba sa ba mata kulawar da ta dace. Kowace jam’iyya cike take da rashin haɗin kai da rashin tsayayyar manufa kan ci gaban al’umma. Mun ga cewa NDP tana da manufofi masu inganci da za su kawo ci gaban da muke fata,” inji ta.
Ta ce suna da ƙwarin gwiwar lashe zaɓe, domin mata su ne ginshiƙi da tushen al’umma, kuma su ne suka fi fitowa a lokacin zaɓe.
Game da yadda ta tsinci kanta a takarar, mataimakiyar ’yar takarar gwamnan, Ambasada Sameera, ta ce gwagwarmayar siyasa ce ta kai ta ga wannan matsayi.
“Na taɓa neman tsayawa takara a Kano ta Tsakiya a lokacin da nake ADC. Daga baya aka samu rabuwa, wasu suka koma NDC. Shi ya sa na koma NDP saboda kyawawan manufofinta, sannan aka ga na cancanta kuma aka zaɓe ni a matsayin mataimakiyar ’yar takarar gwamna,” inji ta.
Ta bayyana cewa manyan manufofinsu idan Allah ya ba su nasara sun haɗa da bunƙasa ci gaban matasa, inganta tsarin karatun Almajirai da kuma bunƙasa ilimin yara da matasa, domin ilimi shi ne ƙashin bayan ci gaban al’umma.
Ta ƙara da cewa za su mayar da hankali wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, ta hanyar tarbiyyantar da matasa da kuma karkatar da su zuwa ayyukan da za su amfanar da rayuwarsu da al’umma baki ɗaya.
Ambasada Sameera ta kuma bayyana cewa za su ba mata masu aure da zawarawa kulawa ta musamman, ta hanyar koyar da su sana’o’in dogaro da kai domin su riƙa kula da kansu da iyalansu cikin sauƙi.
“Gwamnatin NDP idan ta kafa gwamnati, ba za ta tsaya kan gina gadoji da hanyoyi kawai domin ƙawata tituna ba, kamar yadda wasu gwamnatoci suke yi. Za ta aiwatar da ayyukan da za su shafi rayuwar talaka kai tsaye, tare da magance matsalar tsaro tun daga tushe,” in ji ta.
Ambasada Hajiya Sameera Bala Usman ta yi kira ga al’ummar Jihar Kano, musamman matasa da mata, da su ba jam’iyyar NDP cikakkiyar goyon baya domin samun nasara a zaɓen shekarar 2027.
