
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar APC ta zargi tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da jam’iyyar ADC da yunƙurin ɓata kimar taron gangamin buɗe yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da aka shirya a yau Asabar, 24 ga Oktoba, 2026.
A wata sanarwa da Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC, Dele Alake ya fitar a ranar Asabar, jam’iyyar mai mulki ta yi zargin cewa Atiku da jam’iyyarsa ta ADC sun shirya ruɗar da jama’a da ƙoƙarin rage kimar gangamin ta hanyar abin da ya kira da ayyukan labarin ƙarya ciki har da amfani da fasahar AI, bidiyoyin bogi da takardun bogi. A cewar sanarwar, an shirya haka ne da nufin zubar da kimar taron APCn na Kaduna, Shugaba Bola Tinubu, Gwamna Uba Sani na Kaduna da wasu jagororin jam’iyyar mai mulki.
A cewar kakakin, ba yadda za a yi wata jiha a Nijeriya ta kashe zunzurutun kuɗi har tiriliyan N2.3 akan wani taron siyasa. Ya ce, kuɗin wanda Atiku da abokansa suka yaɗa wa al’umma, ya kere kasafin jihar Kaduna na shekara uku.
Kwamitin yaƙin neman zaɓen ya yi iƙirarin cewa an baza wasu daga cikin salon cikin sa’o’i 24 kafin taron domin ruɗar da jama’ar ƙasa, waɗanda suka fara da fitar da hotunan da ke nuna motocin jami’an tsaro na sintiri da aka jibge a kusa da wasu allunan tallar takarar ‘yan APC a cikin garin Kaduna. APC ta yi zargin cewa, an yaɗa farfagandar Atiku da ADC da ƙoƙarin hargitsa al’amura ta hanyar amfani da hotunan wajen iƙirarin cewa an jibge jami’an tsaro ne domin su bai wa allunan tallar ‘yan takarar APCn a Kaduna kariya.
Haka kuma, sanarwar ta yi zargin cewa an yi amfani da wata jaridar ƙasa domin yaɗa manufar, wadda kwamitin APC-PCC ya bayyana a matsayin mai sashen da ke adawa da gwamnati da kuma jam’iyyar APC. A cewar APC, jim-kaɗan bayan jaridar ta wallafa abin da ta kira da rahoton ƙarya, Atiku ya wallafa labarin a sahihan shafukansa na Soshiyal Mediya domin tayar da ƙura acikin al’umma.
Kazalika, kwamitin ya yi zargin cewa bayan faruwar haka ne Atiku da abokansa na ADC suka sake fitar da wata wasiƙa a kafafen sada zumunta da ke baynin cewa, wai Gwamna Uba Sani na Kaduna ne ya rubuta ta ga Abdulaziz Yari, Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen APC, inda aciki, aka yi iƙirarin cewa Gwamnatin jihar ta ware Naira tiriliyan 2.3 domin jagorantar gangamin APCn. Saidai, jam’iyyar APC ta ƙaryata wannan iƙirari tare da cewa hakan abu ne da hankali ba zai iya ɗauka ba, tana mai ƙalubalantar ɓangarorin da su kare iƙirarin nasu da hujjar da za ta iya gamsar da al’umma.
A cewar kakakin ba yadda za a yi wata jiha a Nijeriya ta kashe zunzurutun kuɗi har tiriliyan N2.3 akan wani taron siyasa. Ya ce, kuɗin wanda Atiku da abokansa suka yaɗa wa al’umma, ya kere kasafin jihar Kaduna na shekara uku. Ya bayyana cewa kuɗin kasafin jihar na 2024 biliyan N458.271 ne, sannan biliyan N790.439 ga na 2025 da kuma N985.9 biliyan ga na 2026, wanda jimillar hakan bai kai tiriliyan N2.3, yaan mai kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da zancen marsa asali sannan su riƙa amfani da sahihan kafafen labarai wajen yarda da muhimman batutuwa.
