2027: Tsohon Sufeton ’Yan Sanda ne zai lashe zaɓen gwamnan Nasarawa – Ali Bagio

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Jibrin Ali, wanda aka fi sani da Ali Bagio, kuma babban mai goyon baya da mai tara ƙuri’u na musamman na ɗan takarar kujerar gwamnan Jihar Nasarawa a ƙarƙashin Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Alhaji Abubakar Mohammed Adamu, ya bayyana cewa ɗan takararsu ne kaɗai zai iya lashe zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a shekarar 2027.

Bagio ya bayyana hakan ne a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, yayin wata tattaunawa ta musamman da manema labarai kwanan nan.

Ya musanta rahotannin da ke cewa ɗan takarar SDP da aka zaɓa kafin shigowar Abubakar Mohammed Adamu cikin jam’iyyar ya ƙi janyewa domin bai wa tsohon IGP damar tsayawa takara, yana mai cewa wannan zargi ba gaskiya ba ne, illa dai ƙoƙari ne na tayar da rikici da rudani a cikin jam’iyyar.

Mai yaƙin neman ƙuri’u na Abubakar Mohammed Adamu ya kuma musanta zargin cewa magoya bayan tsohon IGP ne ke haddasa rikice-rikice a jihar. A maimakon haka, ya zargi wasu daga cikin masu fada-a-ji na jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) mai mulki da magoya bayanta da haddasa rikicin siyasar jihar.

Jibrin Ali Bagio ya kuma yi nuni da sakamakon zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka gudanar kwanan nan, yana mai cewa rashin nasarar APC a zaɓen wata alama ce ta abin da zai iya faruwa a Jihar Nasarawa a zaɓen 2027.

“Rushewar APC a Osun ita ce gwajin da zai nuna abin da zai faru a Jihar Nasarawa a 2027, insha Allah, inda jam’iyyar APC mai mulki za ta sha kashi ita ma a hannun ɗan takararmu a nan Jihar Nasarawa,” inji shi.

Bagio ya yi kira ga magoya bayan SDP a faɗin jihar da su fito da yawa, tare da tabbatar da cewa sun mallaki katin zaɓe na dindindin (PɓC), domin su samu damar kaɗa ƙuri’a mai yawa ga Abubakar Mohammed Adamu a ranar zaɓe.

Ya ce yana da yakinin cewa nasarar tsohon IGP za ta kawo sabon salo na shugabanci a Jihar Nasarawa, yana mai cewa tarihin Abubakar Mohammed Adamu na hidima ga al’umma ba tare da nuna bambancin addini, siyasa ko ƙabila ba ya sanya shi cancantar jagorantar jihar.

A ƙarshe, Bagio ya tabbatar wa al’ummar Jihar Nasarawa cewa ba za su yi nadamar ba da ƙuri’unsu ga tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Nijeriya ba, yana mai cewa idan aka ba shi damar jagorantar jihar, “tabbas makomar jihar ta tabbata,” inji shi.

By ukarofi

Leave a Reply