Da Tinubu ya so da na taimaka masa APC ta lashe zaɓen Osun ‘ko ta halin ƙaƙa’  — Wike

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi amfani da cikakken tasirinsa na siyasa wajen zaɓen Gwamnan Jihar Osun, da jam’iyyar APC ta lashe zaɓen.

Wike, wanda har yanzu yake cikin jam’iyyar adawa ta PDP amma yana goyon bayan gwamnatin Tinubu, ya bayyana cewa Shugaban ƙasar ya bar zaɓen ya gudana ba tare da amfani da ƙarfin Gwamnatin Tarayya wajen neman nasarar APC ba.

Wike ya bayyana hakan ne yayin da yake duba wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a Maitama, Abuja, inda ya ce da Shugaba Tinubu yana son APC ta lashe zaɓen Osun ko ta halin kaka, da shi da kansa ya jagoranci ƙoƙarin tabbatar da nasarar.

“Da Shugaban ƙasa yana son lashe zaɓen Osun ko ta halin kaka, da na kasance a can, kuma da mun lashe shi. Babu abin da gwamnan zai iya yi,” inji Wike.

Ya ƙara da cewa ba a yi amfani da “ƙarfin Gwamnatin Tarayya” wajen zaɓen ba.

A zaɓen da aka gudanar ranar 15 ga Agusta, Gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord ya lashe ƙananan hukumomi 19 cikin 30, yayin da ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, ya samu nasara a ƙananan hukumomi 11.

Wike ya kuma ce da abubuwa sun tafi yadda ya kamata, da Adeleke yana cikin jam’iyyar APC.

Ministan ya yi hasashen cewa zaɓen shugaban ƙasa na 2027 zai fi sauƙi ga Shugaba Tinubu idan aka kwatanta da na 2023, yana mai cewa jam’iyyun adawa sun raunana.

Ya ce: “Zaɓen 2027 zai kasance mafi sauƙi ga Shugaban ƙasa idan aka kwatanta da 2023. A wannan karon, an raunana ’yan adawa, ba su da gida, ba su da gashin tsuntsu.”

A wani ɓangare na ayyukan da yake gudanarwa a Abuja, Wike ya duba aikin Inner Southern Eɗpressway (Goodluck Jonathan Way) da hanyoyin gefe na Southern Parkway a Gaduwa, inda ya tabbatar da cewa ana sa ran kammala ayyukan zuwa ƙarshen Disamba 2026 ko farkon Janairu 2027.

Ya ce kammala ayyukan zai taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa da inganta zirga-zirga tsakanin sassa daban-daban na Babban Birnin Tarayya.

Wike ya yaba wa kamfanin China Geo-Engineering Corporation (CGC), wanda ke gudanar da aikin, bisa ci gaba da aiki dare da rana, yana mai cewa sakin kuɗaɗen aikin da Gwamnatin Tarayya ta yi bisa amincewar Shugaba Tinubu ya taimaka wajen saurin aikin.

Ya kuma bayyana cewa matasan al’ummomin da ke kewaye da wuraren aikin na samun ayyukan yi, lamarin da ya taimaka wajen samar da zaman lafiya a yankunan.

Wike ya ce cikin shekaru uku da suka gabata, Gwamnatin FCT ta sanya hannu kan takardun mallakar filaye guda 26,272, idan aka kwatanta da kusan 7,000 da gwamnatocin baya biyu suka bayar cikin shekaru 13.

Ya ce duk da cewa har yanzu akwai matsaloli a Abuja, ba za a iya musanta irin ayyukan ci gaban da gwamnatin yanzu ta aiwatar ba.

A yayin ziyarar, Wike ya bayar da umarnin rushe duk gidaje da gine-ginen da aka gina a kan hanyoyin ruwa a Maitama da sauran wuraren da ambaliya ta fi barazana.

Ya umarci sashen Deɓelopment Control da ya fara rushe gine-ginen nan take tare da kammala aikin zuwa Asabar, yana mai cewa ba matsayin mai gida ko yanayin siyasa da ake ciki zai hana aiwatar da dokokin tsara birane ba.

“Za mu rushe duk gidajen da aka gano an gina su a kan hanyar ruwa. Wasu daga cikinsu na ’yan majalisar dattawa ne, wasu kuma manyan mutane ne,” in ji shi.

Ministan ya ce binciken da aka gudanar bayan ambaliyar da ta faru a Abuja ya nuna cewa wasu masu gidaje sun toshe hanyoyin da aka tanada a Abuja Master Plan domin fitar da ruwan sama.

Ya bayyana gina gine-gine a kan hanyoyin ruwa, toshe magudanan ruwa, zubar da shara ba bisa ka’ida ba da kuma rashin share magudanan ruwa a matsayin wasu daga cikin abubuwan da ke ƙara tsananta ambaliyar ruwa a Abuja.

Ya kuma umarci a gaggauta share magudanan ruwa da aka gano suna buƙatar gyara, tare da yin kira ga mazauna Abuja da ’yan kasuwa da su daina zubar da shara a magudanan ruwa.

Wike ya amince cewa sauyin yanayi da yawan ruwan sama na daga cikin abubuwan da ke haddasa ambaliya, amma ya ce ayyukan ɗan Adam ma suna ƙara ta’azzara matsalar.

Ya kuma ba da umarnin kare wuraren da aka ware domin ciyayi da bishiyoyi daga mayar da su wasu wuraren amfani ba bisa ka’ida ba, yana mai jaddada cewa ba zai dakatar da aiwatar da dokokin tsara birane saboda zaɓe ko siyasa ba.

By ukarofi

Leave a Reply