
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata ‘yar asalin Jihar Gombe mai suna Maryam Ibrahim Ɗan’azumi ta yi nasarar lashe gasar Musabaƙar karatun Al-Ƙur’ani Mai Girma na Sarki Abdulaziz karo na 46 da aka gudanar a ƙasa Mai tsarki ta Saudiyya.
Maryam, wadda ɗaliba ce a makarantar Abubakar Siddiq Community Islamic School for Quranic Memorisation, da ke unguwar Herwagana a cikin garin Gombe, ta wakilci Nijeriya ne a gasar a rukunin mahaddata Ƙur’ani izufi 60, Tajwidi da Tafsirinsa.
Ta yi nasarar zuwa ta ɗaya a cikin ɗalibai daga ƙasashe da dama, abin alfaharin da ya biyo bayan hazaƙa da ƙoƙarinta da ya kai ga ɗaga sunan Jihar Gombe da Nijeriya a idon duniyar Musulunci.
Wannan nasara ta kasance mai muhimmanci a gasar karo na 46, wanda kuma shi ne na farko da aka taɓa ba wa mata damar shiga a tsawon shekaru 46 da aka shafe ana gudanarwa a ƙasar.
Da yake tsokaci kan haka, Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya taya Maryam, iyalanta, malamai da baki ɗaya al’ummar Musulmin jihar murna, yana mai bayyana nasarar a matsayin abin alfahari ga Gombe da Nijeriya.
A wata sanarwa da Daraktan harkokin labaransa, Ismaila Misilli ya fitar, gwamnan ya ce ɗalibar ta samu nasarar ne bisa horo, sadaukarwa da ƙoƙarin koyon karatu, yana mai cewa samun irin haka a matakin ƙasa-da-kasa yana nuna ƙarfin baiwa da ƙwarin-gwiwa acikin matasan jihar.
