Tinubu ya buɗe yaƙin naman zaɓe da caccakar ‘yan adawa, ya kira Aregbesola da ‘rabin albashi’, Atiku kuma ‘jahili’

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da aka kaɗa gangar siyasar zaɓukan 2027, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buɗe yaƙin neman zaɓensa da caccakar ‘yan adawa, inda ya soki tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola da tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar kan matsayar siyasa.

Tinubu ya yi waɗannan kalamai ne a ranar Alhamis yayin karɓar baƙuncin Gwamna Ademola Adeleke a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, kwanaki kaɗan da Adeleke ya sake lashe zaɓen gwamnan Osun da aka gudanar a ranar 15 ga Agusta.

A ranar 19 ga Agusta ne aka fara yaƙin neman zaɓen tsaya wa takarar shugaban ƙasa da ‘yan majalisar dokokin ƙasa a hukumance a Nijeriya, inda ake fafutukar neman ƙuri’un ‘yan Nijeriya tsakanin Shugaba Tinubu da abokan hamayyarsa irin su Atiku na ADC, Peter Obi na NDC da makamantansu.

Yayin tsokaci game da alƙawarin Atiku na dawo da tallafin fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaba a 2027, Tinubu ya bayyana hakan a matsayin hujja da ke nuna “matuƙar jahilci” kan shugabanci da tattali.

“Na ga ɗaya daga cikin abokan hamayyata, Atiku Abubakar, yanzu yana cewa zai koma wa tallafi. Na karanta haka,” inji Tinubu. Ya ce: “Wannan nuna tsantsar jahilci ne akan shugabanci da tattali. Kafin na zo nan, jihohi 27 ba sa iya biyan albashi, ba ma a yin maganar ‘yan fansho, albashin ma’aikata.”

Haka kuma shugaban ya yi amfani da damar wajen caccakar Aregbesola, wanda ya yi gwamna a Osun daga 2010 zuwa 2018, inda ya ce “a jiharka, na san wani mutum da na raina wanda ake wa laƙabi da rabin albashi.” Shugaban ya alaƙanta laƙabin “Half Salary” ne da gwamnatin Aregbesola, wadda ta fuskanci ƙalubale wajen biyan ma’aikatanta cikakken albashi.

A cewar Tinubu, matsin rashin wadatar kuɗaɗe da jihohi suke fuskanta a baya na daga cikin dalilan da suka sa shi ɗaukar matakin cire tallafin fetur a lokacin da ya kama aiki a Mayun 2023.

By Babaji

Leave a Reply