Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Ƙungiyar ma’aikatan ayyukan jin ƙai wato Social Workers a turance ta Najeriya reshen jihar Nasarawa ta yaba wa Gimbiya Dr. Margaret Elayo kwamishiniyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa bisa jajircewarta wajen magance matsalolin muhalli da gaskiya da ƙarfin gwiwa musamman ambaliyar ruwa a yanzu da damina ta yi nisa.
Ƙungiyar ta gabatar da wannan yabo ne yayin ziyarar girmamawa da shugabannin reshen jihar suka kai wa kwamishinan a ofishinta da ke Lafia babban birnin jihar.
Da yake jawabi shugaban ƙungiyar a jihar Nasarawa Prince Ogiri Gambo Adamu ya ce manufar ziyarar tasu ita ce ƙara ƙarfafa haɗin kai da kwamishiniyar wadda aka sani a matsayin mai fafutukar kare ayyukan jin ƙai a faɗin jihar baki ɗaya.
Prince Adamu ya yaba da jajircewa da ayyukan cigaba da Dr. Margaret ke nunawa wajen magance matsalar ambaliyar ruwan da ta shafi mazauna birnin Lafiya da kewayen ta da ma sauran sassan jihar baki ɗaya. Kwamishiniyar ta cancanci yabo ba zagi ba bisa ƙoƙarin da take yi inda ya buƙaci ta cigaba da hakan sannan ya yi kira ga ma’aikatan ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasar su cigaba da bata cikakken goyon baya don bata damar cigaba da ayyukan agajin.
A nata ɓangaren da take mayar da jawabi kwamishiniyar Dr. Margaret Elayo ta nuna godiyarta ga ƙungiyar inda ta buƙaci ƙungiyar da ta cigaba da taimakawa wajen wayar da kan jama’a kan illar zubar da sharar gida ba bisa ƙa’ida ba da gina gidaje a kan hanyoyin ruwa da sauran su don guje wa aukuwar ambaliyar da sauran bala’oin da ke tattare da muhalli a jihar.
Wakilin mu a jihar ya kuma ruwaito cewa a lokacin ziyarar ta musamman, ƙungiyar ta kuma gabatar da kyautar gogaya da jakar sharar gida da sauran su ga kwamishiniyar domin taimakawa ƙoƙarin ma’aikatar wajen inganta tsafta.
