Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a Jihar Nasarawa kuma shugaban Inter-Party Advisory Council (IPAC) na jihar, Hon. Danlami Mohammed Musa, ya nesanta kansa da sauya sheƙar wasu ’yan Majalisar Dokokin Jihar ta Nasarawa zuwa jam’iyyar, yana mai cewa ba a bi ƙa’idar da ta dace ba wajen shigar da su jam’iyyar.
’Yan majalisar da abin ya shafa sun haɗa da Jacob Kudu mai wakiltar Nasarawa Eggon East da Mohammed Adamu Omadefu mai wakiltar Keana, waɗanda suka fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Kakakin Majalisar, Dr. Danladi Jatau, ne ya sanar da sauya sheƙar tasu yayin zaman majalisar.
Danlami Musa ya ce bai karɓi waɗannan ’yan majalisar a matsayin sababbin mambobin SDP ba, saboda ba su tuntuɓe shi a matsayinsa na shugaban jam’iyyar na jihar ba.
“Ina jin labari ne kawai ta rediyo cewa sun sanar a zauren majalisar cewa sun sauya sheƙa zuwa SDP. Ban karɓe su ba, kuma ba su da takardar zama mambobin jam’iyyar daga wurina,” inji shi.
Ya ƙara da cewa duk wani ƙudiri da ’yan majalisar za su gabatar a matsayin mambobin SDP ba zai ɗaure shugabancin jam’iyyar ba, saboda ba a bi tsarin da ya dace wajen shigar da su ba.
A wani ɓangare, Musa ya ce jam’iyyar ta kori Hon. Solomon Akwashiki, mai wakiltar Lafia Central kuma Minority Whip na Majalisar, bisa zargin ayyukan da suka saɓa wa jam’iyya.
Ya zargi Akwashiki da yin kamfen a fili domin neman goyon bayan tsohon Ministan Yaɗa Labarai, Solomon Ewuga, a zaɓen cike gurbin kujerar Sanatan Nasarawa ta Arewa da aka gudanar a baya. Musa ya kuma ce Akwashiki ba ɗan takarar SDP ba ne a kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Lafia/Obi.
Sai dai Akwashiki ya musanta zargin korar tasa daga jam’iyyar, yana mai cewa matakin ba shi da tushe.
Ya ce ɗanlami Musa ba shi da hurumin dakatar da shi ko korar sa daga SDP, domin ba shi ne shugaban jam’iyyar na jihar ba. A cewarsa, Barrister Ajegena Illiya ne halastaccen shugaban SDP na Nasarawa, wanda ya samu nasara a wani babban taron jam’iyyar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) suka sanya ido a kai.
Akwashiki ya ce sunansa yana cikin jerin ’yan takarar da INEC ta wallafa domin zaɓen 2027, yayin da sunan ɗanlami Musa bai cikin jerin ’yan takarar gwamna na SDP ba.
Ya ce: “Ni ɗan takarar SDP ne. INEC ta sanya sunana cikin waɗanda za su fafata a zaɓen 2027. Sunansa ba ya cikin jerin. Ya kamata ya daina gabatar da kansa a matsayin shugaban jam’iyyar.”
Ya kuma tabbatar da cewa Hon. Mohammed Omadefu da Hon. Jacob Kudu sun shiga SDP, tare da gargaɗin cewa jam’iyyar za ta ɗauki matakin shari’a kan ɗanlami Musa bisa zargin yin kamar shi ne shugaban jam’iyyar.
