Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kimar Naira na ci gaba da samun tagomashi, yayin da tazarar farashinta tsakanin kasuwar hukuma da ’yan canjin kuɗi ta ragu zuwa ƙasa da kashi biyu cikin 100.
A halin da ake ciki, Asusun Ajiyar ƙasar Waje na Nijeriya ya haura dala biliyan 52.5 zuwa ranar 17 ga Yuli, 2026, matakin da ya kai mafi girma cikin shekaru 17, tare da zarce burin shekara-shekara da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanya.
CBN ya ce, wannan ƙaruwa ta samu ne sakamakon ci gaba da shigowar kuɗaɗen waje cikin ƙasar da kuma sake farfaɗowar amincewar masu zuba jari da shigarsu sassa daban-daban na tattalin arzikin Nijeriya.
Muƙaddashiyar Daraktar Sashen Sadarwa da Hulɗa da Masu Zuba Jari na CBN, Hakama Sidi-Ali, ce ta bayyana hakan a ranar Talata a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, yayin wani baje kolin da babban bankin ya shirya, wanda ya samu halartar mutane daga sassa daban-daban na jihar.
Sidi-Ali ta bayyana cewa cikin watanni 34 da suka gabata, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya jagoranci wasu manyan sauye-sauye da nufin kafa tubalin da zai tallafa wa sabon zangon ci gaban tattalin arzikin Nijeriya, tare da bunƙasa tattalin arziki mai amfani ga kowa da kuma samar da ayyukan yi domin rage talauci.
Ta ce daga cikin sauye-sauyen akwai haɗa kasuwar canjin kuɗin waje wuri guda da kuma ƙara bayyana gaskiya a harkokinta; da kuma nasarar sake ƙarfafa jarin bankunan kasuwanci, wanda a cewarta ya inganta ƙarfin jure matsaloli, ƙwarewa da gogayyar harkar banki a Nijeriya.
Sauran sauye-sauyen sun haɗa da ƙaddamar da BVN ga ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje, domin haɗa su da ayyukan bankuna a gida; ƙaddamar da Tsarin B-Match na hada-hadar canjin kuɗin waje; bayyana Tsarin hangen nesa na tsarin biyan kuɗaɗen Nijeriya na 2028; da kuma ɗora kashi 75 cikin 100 na Cash Reserve Ratio kan ajiyar kuɗaɗen ɓangaren gwamnati da ba sa cikin Asusun Bai ɗaya na Baitulmalin Tarayya (TSA), domin inganta kula da kuɗaɗen da ke yawo da kuma rage haɗarin hauhawar farashi.
Sidi-Ali ta ce sabbin alƙaluman Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) sun nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya ta ragu kaɗan, daga kashi 15.91 a watan Yuni zuwa 15.43 a watan Yuli na 2026.
Ta ce, hauhawar farashin kayayyakin abinci da kuma hauhawar farashin da ba na abinci ba su ma sun ragu a wannan lokaci, abin da ta danganta da tsauraran matakan manufofin kuɗi, haɗa kasuwar canjin kuɗi da kuma ƙara gaskiya a kasuwa.
Da take magana kan taken baje kolin, “Amfani da Madadin Hanyoyin Biyan Kuɗi a Matsayin Kayan Haɓaka Shigar da Jama’a Tsarin Kuɗi, Ci Gaban Tattalin Arziki da Gaggauta Bunƙasa ƙasa,” Sidi-Ali ta ce an zaɓi taken ne domin nuna alaƙar da ke tsakanin waɗannan muhimman fannoni da samun daidaiton harkokin kuɗi, farashi da tsarin hada-hadar kuɗi, waɗanda suke cikin manyan manufofin CBN. Ta bayyana baje kolin a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin da bankin ke amfani da su wajen wayar da kan jama’a game da manufofinsa da shirye-shiryensa, tare da manufar bunƙasa tattalin arzikin ƙasa cikin ɗorewa.
Sidi-Ali ta kuma yi kira ga jama’a su riƙa girmama Naira da kiyaye tsaftarta, tana mai jan hankali cewa fesa kuɗi a wuraren taro, sayar da Naira a titi, yaga ko lalata ta, da kuma ƙirƙirar jabun kuɗi duk haramtattu ne. Ta ce Naira ba wai alamar ƙasa ce kawai ba, har ila yau tana wakiltar abin alfaharin ’yan Nijeriya baki ɗaya.
