Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani sabon bincike ya nuna cewa amfani da ƙirƙirarriyar basira ta AI na iya taimaka wa ƙananan da matsakaitan ’yan kasuwa a Nijeriya wajen inganta aiki, rage kashe kuɗaɗen gudanarwa da kuma ƙara musu damar gogayya a kasuwa.
Binciken, wanda Dr Ayodeji Idowu ya gudanar kuma aka wallafa a International Journal of Comparative Studies in International Relations and Development, ya ce ci gaban fasahar ajiyar bayanai a ma’adana, wato cloud computing, dandamalin zamani masu sauƙin amfani da kuma API ya rage wahalar da ƙananan kamfanoni ke fuskanta wajen rungumar fasahar AI.
Masanin ya bayyana cewa ƙananan da matsakaitan ’yan kasuwa ba sa buƙatar zuba maƙudan kuɗaɗe ko ɗaukar ƙwararrun masana kimiyyar bayanai kafin su fara amfani da AI a fannoni kamar kula da kwastomomi, tallace-tallace, harkokin kuɗi da gudanar da ayyukan kasuwanci.
Binciken ya nuna cewa AI na iya sarrafa amsoshin tambayoyin kwastomomi, nazarin yanayin kasuwa, inganta sarrafa hajojin kasuwanci da kuma tafiyar da tsarin lissafin kuɗi, wanda zai rage kuskuren da ake samu sakamakon aikin hannu tare da taimaka wa ’yan kasuwa wajen yanke shawara mai inganci.
Haka kuma, kamfanonin sufuri da rarraba kaya za su iya amfani da AI wajen tsara hanyoyin kai kaya mafi inganci, rage yawan man fetur da inganta ayyukansu. Masu sayar da kaya kuma za su iya amfani da nazarin hasashen kasuwa domin fahimtar halayen masu saye da kuma ƙara yawan ciniki.
Binciken ya kawo misalan wasu kamfanoni na ƙasashen waje da suka samu nasara bayan rungumar AI. Daga cikinsu akwai TKG, wani kamfanin masana’antu na iyali a Jamus, wanda ya rage lokacin sarrafa odar kaya da fiye da kashi 50 cikin 100 bayan haɗa AI cikin ayyukansa. Binciken ya ce kamfanin ya kuma dawo da kuɗin da ya zuba wajen wannan fasaha cikin ƙasa da shekaru uku.
Haka kuma, an ambaci wasu ’yan kasuwa da suka yi amfani da tsarin AI na hasashen halayen masu saye, inda aka samu ƙarin tallace-tallace da kusan kashi 25 cikin 100 a cikin kwata guda.
Sai dai Dr Idowu ya bayyana cewa akwai wasu manyan ƙalubale da ke hana ƙananan da matsakaitan ’yan kasuwa a Nijeriya rungumar AI. Ya lissafa ƙarancin ƙwarewar fasahar zamani, rashin fahimta kan kuɗin aiwatar da AI, matsalar wutar lantarki, rashin ingantaccen intanet da kuma ƙin sauya tsoffin hanyoyin aiki a matsayin manyan matsalolin.
Binciken ya gano cewa kusan kashi 65 cikin 100 na ƙananan da matsakaitan ’yan kasuwa na kallon ƙarancin ƙwarewar fasaha a matsayin babban cikas ga rungumar fasahohin zamani.
Domin magance matsalolin, masanin ya bayar da shawarar ’yan kasuwa su rungumi AI a hankali, su fara da gano inda fasahar za ta fi amfani ga kasuwancinsu, sannan su yi amfani da shirye-shiryen AI da ake samu a kasuwa cikin sauƙi.
Ya kuma shawarci ’yan kasuwa su fara amfani da AI wajen ayyukan ofis da ake maimaitawa, su inganta ilimin ma’aikatansu kan fasahar zamani, sannan daga baya su koma amfani da tsarin AI na musamman yayin da ƙwarewarsu ta bunƙasa. Dr Idowu ya kuma yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnati, kamfanonin fasaha, cibiyoyin ilimi da ’yan kasuwa domin hanzarta yaɗuwar amfani da AI a harkokin ƙananan da matsakaitan kasuwanci.
