Babu shugaban da ya sauya tarihin Nijeriya kamar IBB — Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu wani shugaban ƙasa da ya taka rawa wajen sauya tarihin Nijeriya kamar tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya).

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin saƙonsa na taya tsohon shugaban ƙasar murnar cika shekaru 85 da haihuwa.

A cikin sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana Babangida a matsayin fitaccen shugaba, wanda ƙwarewarsa a aikin soja ta kai ga zama shugaban ƙasa bayan juyin mulkin 1985.

Shugaban ya ce ko mutum yana son Babangida ko ba ya sonsa, Nijeriya ta tasirantu da mulkinsa ta hanyoyin da babu wani shugaba da ya taɓa yi.

Ya ce mulkin Babangida na tsawon shekaru takwas ya bar tarihi mai ɗorewa a fannonin siyasa, tattalin arziki da tsarin jihohin ƙasar.

A cewar Tinubu, Babangida ya faɗaɗa tattalin arzikin ƙasa, ya samar da muhimman ababen more rayuwa da suka daɗe suna amfani, tare da kafa hukumomi da cibiyoyi da dama waɗanda har yanzu suke hidima ga muradun ƙasa.

Ya ce: “Ba don hangen nesansa, hikimarsa da fahimtarsa ta adalci da daidaito ba, da akwai yiwuwar wasu jihohin da ba su wanzu ba.”

Tinubu ya ce sunan Babangida da tarihin gudunmawar da ya bayar ga Nijeriya za su ci gaba da kasancewa cikin tarihin ƙasar saboda irin rawar da ya taka wajen ci gabanta.

Ya kuma ce ko bayan ritayarsa, inda yake rayuwa cikin nutsuwa a gidansa da ke kan tsauni a birnin Minna na Jihar Neja, Janar Babangida na ci gaba da bai wa ƙasa shawarwari masu amfani.

“Shawarwarinsa da hikimarsa na ci gaba da zama abin koyi da ƙarfafa gwiwar matasa,” inji Shugaba Tinubu.

Tinubu ya ƙara da cewa: “Ina yi maka fatan samun ƙarin falala, lafiya da ƙarfi. Allah Maɗaukaki Ya ci gaba da kiyaye ka tare da mu na tsawon shekaru masu yawa.”

By ukarofi

Leave a Reply