Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Farashin kayayyakin masarufi ya ƙaru a watan Yuli a Nijeriya, duk da matakan da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka domin bunƙasa samar da kayayyaki a cikin gida da rage kuɗin sarrafa su, da nufin sauƙaƙa wa ’yan ƙasa halin tsadar kayan abinci.
Hauhawar farashin ta haifar da damuwa game da tasirin matakan da gwamnati ke ɗauka domin samar da sauƙi a farashin kayan abinci.
Sabbin alƙaluman da Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar sun nuna cewa farashin kayan abinci ya ƙaru da kashi 20.31 cikin 100 cikin watanni 12 da suka gabata.
Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ta tashi daga kashi 1.82 cikin 100 a watan Yuni zuwa kashi 3.75 cikin 100 a watan Yulin 2026.
Rahoton ya kuma nuna cewa farashin kayayyaki ya ci gaba da hauhawa a watan Yuli, duk da cewa hauhawar farashin ta shekara-shekara ta ragu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Jihohin da aka samu mafi yawan hauhawar farashin kayan abinci sun haɗa da Adamawa da kashi 17.02 cikin 100 da Legas da kashi 13.48 cikin 100.
Sai dai an samu raguwar farashin kayan abinci a wasu jihohi, ciki har da Jigawa da kashi -3.68, Kebbi -3.67 da Bauchi -1.85 cikin 100, yayin da Borno ta samu kashi 13.26 cikin 100.
Iyalai da dama dai sun ce har yanzu ba su ga tasirin matakan da gwamnati ta ɗauka wajen rage musu tsadar kayan abinci ba.
Alƙaluman wata-wata da NBS ta fitar sun nuna cewa farashin wasu daga cikin kayan abincin da ake yawan amfani da su, kamar shinkafa, dawa, doya, albasa, fulawa, tumatir da garin kwaki, ya ƙaru.
Yanayin alƙaluman ya nuna cewa farashin kayayyakin ya ƙaru daga watan Yuni zuwa Yuli, duk da cewa saurin tashin farashin bai kai matakin da aka samu a watan Yuni
