Arsenal ta fara kare kambunta na Premier League da lallasa Coventry City

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da aka fara gasar Premier League ta ƙasar Ingila a yammacin ranar Juma’a, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, ta yi nasarar doke Coventry City da ci 3 da 0 a filin wasa na Emirates.

Kai Havertz ne ɗan wasan da ya buɗe asusun zura ƙwallo a gasar ta bana bayan samun wata dama a minti na 15 da take wasan, yayin da Coventry ta gaza jure matsin mai masaukin baƙin.

Wannan ƙwallo ta ba Arsenal damar cigaba da jan ragamar wasan cikin salo mai ban ƙaye kan Coventry, wadda sabuwar ƙungiya ce a gasar da kuma tsohon ɗan wasan Chelsea da Ingila, Frank Lampard ke jagoranta.

A minti na 23 ne Bukayo Saka ya ninka damar bayan gaba-da-gaba da mai tsaron gidan City Carl Rushworth.

Arsenal dai ta cigaba da mamaye wasan, inda bayan minti huɗu da koma wa hutun rabin lokaci, Kyaftin ɗin Gunners Martin Ødegaard ya samu damar zura ƙwallon ƙarshe, lamarin da ya jefa magoya baya cikin farin ciki.

Arsenal dai ita ta lashe Premier League a kakar 2025/2026 bayan shekaru 22 tana dakon kofin, wanda kuma shi ne karo na 14 da ta taɓa lashewa a tarihinta. A wannan kaka ta 2026/2027, ƙungiyar ta fara gasar da ƙafar dama a wani yunƙuri na ƙoƙarin kare kambun nata.

Ƙungiyar ta kuma yi ƙoƙarin ƙarfafa tawagar ‘yan wasanta wajen siyo zaƙaƙuran ‘yan wasa da suka haɗa da Bruno Guimarães, Christos Tzolis da Ezri Konsa daga Aston Villa.

By Babaji

Leave a Reply