Masarautar Koko ta nemi a sauƙaƙa aure

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Mai girma uban ƙasar Koko, Alhaji Mohammed Bello Koko II, ya bayyana aniyar masarautar Koko na farfaɗo da dokokin da za su taimaka wajen sauƙaƙa yin aure ga matasa da kuma masu son ƙara mata ta hanyar rage nauyin kuɗi da al’adun da ke ƙara tsadar aure.

Basaraken ya bayyana cewa tun da farko akwai irin wannan doka a masarautar Koko wacce manufarta ita ce kare matasa daga shiga cikin matsanancin nauyin da zai iya hana su yin aure ko kuma ya sa su fara rayuwar aure cikin matsalolin bashi ko faɗawa tarkon shaiɗan.

Insha Allahu za a dawo da wannan doka kuma za ta fara aiki nan ba da jimawa ba. Ya ƙara da cewa manufar dokar ita ce sauƙaƙa aure da rage almubazzaranci, musamman abubuwan da ba su da muhimmanci ba su da tushe a koyarwar addinin Musulunci da suka yi kutse a cikin harkokin aure.

A cewar sa, ya kamata a koma ga aure mai sauƙi, mai albarka da mutunta iyali, domin aure ba gasar nuna dukiya ba ne, kuma bai kamata tsadar biki ta zama dalilin da zai hana matashi kafa iyali ba.

Ya yi kira ga iyaye da shugabanni a wannan masarautar da sauran masu ruwa da tsaki da su sake duba wadansu al’adu da suka shafi aure musamman abubuwan da ke jawo ƙarin kuɗaɗe da matsin lamba ga iyalai.

Idan aka sauƙaƙa aure, za a taimaka wajen rage yawan jinkirin aure tsakanin matasa, a ƙarfafa zaman iyali, sannan a samar da al’umma mai ɗorewa da tarbiyya.

By ukarofi

Leave a Reply