Wike zai wallafa ayyukan da ya gada daga gwamnatocin baya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Abuja Nyesom Wike, ya sanar da shirinsa na wallafa bayanan ayyukan da ya gada daga gwamnatocin da aka yi a baya da kuma na ayyukan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bai wa gwamnatinsa.

Wike ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan kai ziyarar sanya ido a wasu titina biyu a Abuja, inda ya bayyana gamsuwarsa a kai da kuma ƙwarin aikin da ‘yan kwangilar suke yi.

Ya ce, takardun bayanan za su ƙunshi ayyukan da gwamnatinsu ta gada daga na tsofaffin shugabannin ƙasa da suka haɗa da, Olusegun Obasanjo, Umaru Musa Yar’Adua, Goodluck Ebele Jonathan da kuma Muhammadu Buhari.

A cewarsa, wannan mataki zai ba wa ‘yan Nijeriya damar kamanta ayyuka da suka gada da kammalawa da waɗanda gwamnatinsu ta yanzu ta samar.

A ƙarshe, ya ƙalubalanci dukkan wanda yake da ja akansu, da ya fito ya kare da hujjoji gamsassu yayin da aka wallafa bayanan a ranar Talata ko Laraba na mako mai zuwa kamar yadda ministan ya bayyana.

By Babaji

Leave a Reply