Sabuwar Nijeriya daga 1 ga Oktoba, 2026?

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

Tun bayan shigowar gwamnatin Tinubu ake ta rade-radin cewa akwai yunkuri na maida Najeriya kan tsohon tsarin mulki na shiyyoyi (Regions) wanda aka gwada a shekarun 1960 lokacin su Sardauna, Zik da Awolowo. A halin da ake ciki kuwa an gano wata shawara (proposal) ta sauya fasalin Najeriya (Geo-political zone bill) da ke ta kara-kaina a majalisa wadda Dr Akin Fapohunda ya dau nauyi.

Wannan doka da ake son ganin ta sami karbuwa a majalisa, nan da zuwa 1st ga watan October, ranar da Najeriya ke cika shekaru 66, ake son ta kama aiki.

Ana son shiyyoyin Najeriya guda shida a daidaita su yadda za su zama kowacce shiyya na da jihohi 7, kamar yadda yankin Arewa-maso-yamma ke da jihohi 7. Wadannan shiyyoyi za su zama murhu na hudu (fourth tier) ke nan bayan Federal, state da local government. Ana kuma son saka tsarin a kundin tsarin mulkin Najeriya tare da hana sake kirkirar wata sabuwar jiha bayan samar da jihohi 42. Jihohin za su kasance kenan kamar haka:

Shiyyar Kudu-Maso-Kudu:

Bayelsa State – Yenagoa

West Izon State – Patani

Rivers State – Port Harcourt

Cross River State – Calabar

Akwa Ibom State – Uyo

Edo State – Benin

Delta State – Warri

Shiyyar Arewa-Maso-Gabas:

Mambilla State – Gashaka

Taraba State – Jalingo

Adamawa State – Yola

Borno State – Maiduguri

Yobe State – Damaturu

Bauchi State – Bauchi

Gombe State – Gombe

Shiyyar Kudu-Maso-Gabas:

Anioma State – Asaba

Orashi State – Omoku

Anambra State – Awka

Imo State – Owerri

Enugu State – Enugu

Abia State – Umuahia

Ebonyi State – Abakaliki

Shiyyar Arewa-Maso-Tsakiya:

Abuja State – Abuja

Gurara State – Kafanchan

Benue State – Makurdi

Plateau State – Jos

Nasarawa State – Lafia

Kogi State – Lokoja

Niger State – Minna

Shiyyar Kudu-Maso-Yamma:

Odo Oya State – Ilorin (Kwara)

Oyo State – Ibadan

Ogun State – Abeokuta

Lagos State – Ikeja

Ondo – Akure

Ekiti – Ado-Ekiti

Osun – Oshogbo

Shiyyar Arewa-Maso-Yamma:

Sokoto State – Sokoto

Kebbi State – Birnin Kebbi

Kaduna State – Kaduna

Katsina State – Katsina

Kano State – Kano

Jigawa State – Dutse

Zamfara State – Gusau

A karkashin tsarin za a kawo karshen raba kudade daga asusun tarayya (Federal allocation) a maye gurbinsa da ikon arzikin yankuna (resource control) wanda jihohi za su ci gaba da zama karkashin hadakar tarayya (Federating units) Amma rarraba arziki zai koma Jihohi na da kaso 50% na arzikinsu, Tarayya za ta karbi kaso 20%, Shiyyoyi za su karbi kaso 15% sai asusun gata na tarayya (National Trust Fund) ya karbi kaso 15%.

Wato kowacce shiyya zata sami yancin tsaro da tattalin arzikinta ta daukar alhakin kafa rundunar tsaronta (regional police) wadda zata yi aiki kafada da kafada da rundunar yansanda ta tarayya. Sannan shiyyoyin su za su lalubo hanyoyin samarwa kansu wutar lantarki da rarraba ta. Kowacce shiyya ita zata tsarawa kanta hanyoyi kula da Ilimi, muhalli, sufuri, lafiya da tsaro.

Tuni dama majalisa ta samarwa kowacce shiyya hukumar ci gaban yankin (Development commission). Karkashin wadannan hukumomin za’a rika gudanar da ayyukan shiyyoyin wadda gwamnoni na yanki na ciki kuma za su samar da shugaba (Chairman) wanda za’a rika zagayawa tsakanin jihohi duk shekara. Kwamitin gwamnoni shi ke da ikon zartarwa na ƙarshe.

Wannan sabon tsari zai ba kowacce shiyya damar gudanar da al’amuranta kai tsaye. Kuma kowacce al’umma ya rage na ta wajen ganin ci gaban yankin ta. Wannan yunkuri, ba na zaton zai rasa nasaba da yadda mutanen kudu ke kallonmu a matsayin kaska. Su na ganin cewa mun zama wani waigi da ya ke musu tarnaki wajen ci gaba. Kuma idan za mu yi wa kanmu adalci akwai alamun gaskiya a zancen. Na farko dai mun fi kowa yawan jama’a da rashin aiki da rashin Ilimi da rashin tsaro. Duk da makudan kudade da ake baiwa jihohinmu, a banza don bai bunkasa ma’adinanmu ba, ko noma, ko samar da ayyuka. Shugabanninmu ba ruwansu da talakawa sai gasar mota, mata da gidaje.

Bayan kafa Northwest Development commission, ni da wasu mutane mun yi tattaki mun je mun zauna da shugabanta domin bijiro musu da yadda za a farfado da noma da sana’o’i a yankin Arewa maso yamma. Abin mamakin da Farfesan ya fara gaya mana shine cewa asali biliyan 530 aka warewa hukumar a 2025, kuma ya kama aiki a February, mun same shi a watan September. Amma ba kawai a tsawon wadannan watanni ba a sakar musu budget ba, wasu ne a yankin su ka tafi wajen Tinubu su ka ce wai me za a yi da biliyan 500 a Northwest? Yankin da ya fi kowa talauci da almajirai da rashin tsaro, shi za’a ce me zai yi da biliyan 500?

Daga baya an zaftare wannan Budget zuwa biliyan 140 kuma har shekarar ta kusa fita ba a saki kudaden ba. Su kuma a nasu bangaren, su na shigowa sai su ka fara maganar zasu bada tallafin karatu na neman digiri na biyu. Mun yi ta bibiyarsu da abubuwa har muka gaji domin ba alamar sun shirya. Akwai mutane a England da su ka nemi zuwa su zauna da NWDC domin kulla alaka ta samarwa matasa aiki, wallahi ko bada amsa ta takardar ba su yi ba. Idan ka koma takwararsu ta SWDC kuwa, daya daga cikin abubuwa na farko da su ka yi shine na bijiro da farfado da tsohon layin dogo da ya karade jihohinsu.

Ina bada wannan misali ne domin mu farka mu gane dalilin da ya sa Yan kudu su ka gaji damu, kuma su ke ta kokarin yakice mu. Idan ba mu farka ba har wannan shawara ta karbu, kuma aka aiwatar da ita, wallahi yankin Arewa musamman namu na Northwest sai ya durkushe gaba daya. Wadannan yaran da ke tasowa cikin talauci, jahilci da rashin tarbiya wallahi ba za su bar kowa ya zauna lafiya ba. Musamman la’akari da yadda su ke tasowa da gabar addini da ta kabilanci da son hutu nan take ba tare da wahala ba. Idan mutane irinmu da su ka taso da tarbiya amma a yau akasarinmu mun lalace da son kai da son Duniya da hassada da kyashi, me kake tsammanin gaba ke tanadi da irin yayan da muke tarbiyantarwa a yanzu?

Dabara fa ta rage wa mai shiga rijiya.

Malam Ali manazarci ne a Kano

By ukarofi

Leave a Reply