
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanannen jagoran ‘yan bindiga, Kachallah Muhammad ya tuntubi iyalan Manjo Janar Rabe Abubakar Batsari mai ritaya, wanda aka yi garkuwa da shi tare da matarsa a Jihar Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa, Kachallah Muhammad ya kira iyalan janar din domin tabbatar musu cewa shi da matarsa suna cikin koshin lafiya, duk da cewa har yanzu suna hannun masu garkuwa da su.
An yi awon-gaba da tsohon janar ɗin ne tare da matarsa a ranar Asabar yayin da suke tafiya a hanyar Marabar Musawa zuwa Kafinsoli da ke Karamar Hukumar Matazu a Jihar Katsina, bayan wasu ƴan bindiga sun tare su tare da bude musu wuta kafin su yi awon gaba da su zuwa cikin daji.
Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa an samu damar yin magana kai tsaye da Janar Batsari ta hannun shugaban ƴan bindigar, inda ya tabbatar wa iyalansa cewa babu wata matsala a tare da su.
A yayin tattaunawar, Kachallah Muhammad ya buƙaci hukumomin tsaro su saki wasu daga cikin yaransa da ke tsare, yana mai cewa wannan na daga cikin sharuddan da yake son a bi domin samar da mafita ga lamarin.
Haka kuma, shugaban ‘yan bindigar ya nuna sha’awarsa ta komawa tattaunawar sulhu da nufin samar da zaman lafiya a wasu yankunan da rikicin tsaro ya daɗe yana addaba.
Wannan al’amari ya janyo damuwa acikin al’ummar Katsina da ma sauran ‘yan ƙasa, inda mutane da dama ke kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa domin ceto tsohon jami’in sojan da matarsa cikin koshin lafiya tare da tabbatar da tsaro ga al’ummar Shiyyar Arewa maso Yamma da ma sauran sassa Nijeriya baki ɗaya.
