
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’umma sun girgiza a ranar Talata bayan gano wata gawar wani mutum da aka tsige wa kai a tsohuwar harabar Jami’ar Jos da ke Jihar Filato.
Rahotanni sun bayyana cewa, an yi zargin waɗanda suka halaka shi sun tafi da kan nasa, inda suka bar gangan jikin kaɗai a wajen da aka ƙaddamar da farmakin.
Ɗalibai da dama da ma’aikatan jami’ar ciki har da Shugaban Tsaro, Mista Agama Tangni sun tabbatar da faruwar al’amarin ga manema labarai a Jos, ranar Talata.
A cewar Tangni, sun gano cewa mamacin ba ɗalibi ko ma’aikacin jami’ar ba ne.
Ya bayyana cewa, duk da cewa ba shi da alaƙa ta ɗalibta ko aiki da makarantar, an san wane ne shi saboda yawan halartar wajen da al’amarin ya faru.
Ya ƙara da cewa, alamu sun nuna cewa maharan sun jima suna sanya ido akan zirga-zirgar mamacin gabanin su ƙaddamar da harin.
A cewarsa, an sanar da iyalansa da kuma garzayawa da gawar tasa zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Bingham.
Har zuwa lokacin kammala aikin haɗa wannan rahoto, babu wani saƙo a kai daga rundunar ‘yan sandan jihar a hukumance.
