Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Haƙiƙa har dai mutum zai dubu tarihin haziƙan mata a yankin Arewacin Nijeriya da kewaye, sai ya Ambato sunan haziƙa kuma malama Nana Asma’u ‘yan Shehu Usman Mujaddadi. Abin farin ciki game da Nana shi ne kwarewarta wajen rubutun darussan addinin Musulunci musamman cikin wake. Haƙiƙa mu na da mata a yankin nan da su ka shahara wajen sarauta, jarumtakar yaƙi har kuma a sabon zamani wajen siyasa, tattalin arziki da sauran su, amma ita Nana a kan koyarwar addinin musulunci ta shahara kuma shekaru aru-aru bayan komawarta ga Allah, sunanta ya na nan a raye kamar jiya ko shekarnjiya ta bar duniyar nan. Wani lokacin ma idan mutum ya na ba da tarihinta, sai ya ga idan ma ya shiga Sakkwato zai gan ta ko ma ta na nan a raye a doron duniya. Gaskiya ta rasu ta koma ga Allah amma alherinta na nan a raye daram. Masu sukar rayuwarta don kasancewarta ‘ya ga Mujaddadi, na yin haka ne bias manufar nuna adawa da ayyukan addinin Musulunci. Duk wanda ya dau hanyar bunƙasa ilimi da darsussan addini zai iya gamuwa da ƙalubale daga waɗanda ba sa ƙaunar hakan, ko sun fi so a yi rayuwa irin ta Yammawa.
Na samu dama ni kaina na ziyarci gidan Mujaddadi a Sakkwato inda na isa gaban makwancin Nana Asma’u wanda gaskiya duk mai shauki da ƙaunar Islama ka iya zubar da hawaye don yadda mutanen nan su ka rayu ba don tara komai na jin daɗin duniya ba. Makwancin Nana na nan a ta zagaye bayan makwancin mahaifinta Shehu Mujaddadi kazalika a gefe akwai makwancin Suldanai na Daular Sokoto ciki da waɗanda a sabon zamani a ka fi sani irin Sultan Hassan Dan Mu’azu, Sultan Abubakar na III, Sultan Muhammad Maccido da Sultan Ibrahim Dasuki. Idan mutum ya shiga wannan gida na Shehu zai iya hasko hoton tarihi na gwagwarmayar ƙarfafa Musulunci gabanin zuwan turawan mulkin mallaka da su ka kawo farmaki a 1903.
Akwai sashen ɗaki da muka ziyarta da ke tuna tarihin Nana Asma’u da irin ‘yan kayan tarihi na tasoshi ko ‘yan tukwane da ta yi amfani da su ko a ka adana daga wancan zamanin na Shehu Rahimahullah. Haka rayuwar talikkai ta ke ta na da farko kuma ta na da ƙarshe. Addu’ar duk masu imani farkon ya yi kyau ƙarshen ma ya yi kyau. Ga rayuwar Nana Asma’u sai sambarka don ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen ayyukan da ta gani mahaifanta su na yin a ilimi da koyarwa dare da rana. Gaba da baya ita dai Nana ta fito daga gida na alheri don Baffanta Sheikh Abdullahi Gwandu Balaraben ƙasashen Sudan ya rubuta littattafan Mahadi ka ture kan fannoni na addinin musulunci da a ke amfana da su. Waɗannan bayan Allah fa ba su da lokaci na ƙashin kansu don kullum a cikin hidimar addinin Musulunci su ka rayu har su ka koma ga Allah. Mu ma da mu ke raye yanzu mu na addu’ar dacewa duniya da lahira.
A sabon zamanin nan, akwai wasu mutane waɗanda bincike ya tabbatar ba musulmi ba ne da su ka buɗe shafuka a yanar gizo musamman don aibata Shehu Mujaddadi da iyalinsa da sauran abokan aikinsa na tajdidi. Irin kalaman ɓatanci da murde wuyan tarihin rayuwar Mujaddadi da su ke yi na fito da ajandarsu a fili ta duƙufa wajen yaƙi da Musulunci. Neman tada fitina ne ga wanda ba musulmi ba ya fake da wasu sunaye na bagaye a shafukan yanar gizo don cin zarafin magabata na Musulmi. Duk mai neman kawo irin wannan fitina bai yi dogon tunani ba don ba mutumin da zai iya nasara a yaƙi da addinin Allah. Kuma inda a ke fahimtar mummunar manufar masu wannan kamfen ɗin ba sa bayyana kansu kuma akasari sun kikrkiri sunayen karya da sanya juayyun hotuna da a ka samar ta manhajar AI don yaudarar waɗanda ba su ankara ba.
Na ga wasu ‘yan bazata na martani ga sakon Muhammad I. Alkhizami inda ya ce Nana Asma’u ‘yar Mujaddadi Shehu Danfodiyo ta rubuta sama da littattafai 60 na darussan musulunci; har wani ke nuna marigayiya mawakiya Barmani Choge ta fi ta daraja a wajen Hausawa. Mai martanin da ‘yan uwan kwangilarsa na cewa ai Nana Asma’u wake ta yi don haka wakokin Barmani sun fi na Nana muhimmanci a wajensu. Kafin na yi nisa a nan wa ya ba wa ‘yan karyar Hausa zalla hurumin magana a madadin Hausawa? Mene ne alaƙarsu da Hausa?
A nan ga abu 4 da su ka bayyana:
1. Nana Asma’u gaskiya ne ta rubuta wake kan darussan musulunci don saukin fahimta ga Musulmi kuma sai gwani na gwanaye kan iya juya sako zuwa wake kuma musamman na darussan addini kuma ya fidda cikakkiyar ma’ana. Duk wanda ya muzanta waken addini, kai tsaye ya nuna dama yaƙi ya ke yi da addinin don Musulunci ba layinsa ba ne.
2. Marubutun na zallawa ya yi misali da Barmani Choge don kawai buƙatun misali ne amma bai ma san rayuwar marigayiyar ba kuma a ‘yan shekarunsa cikin cokali ko ta’aziyya bai je na rasuwarta ba amma ya ke da bakin amfani da sunanta don kushe Nana Asma’u bint Fodio.
3. Duk wanda ka ga ya nuna wakokin ‘yan gambara sun fi waken musulunci da Nana ta yi, ba ka buƙatar zurfafa bincike ko shi waye da addinin da ya ke bi.
4. Ba waka ko daya ta Hajiya Barmani Choge har ta koma ga Allah inda ta muzanta Daular Shehu Mujaddadi, hasalima ma mai yabawa ce ga ayyukan alheri da ta taras Mujaddadi da mataimakansa su ka gudanar na ƙarfafa addinin Musulunci a Arewacin Nijeriya da kewaye.
KALUBALE- Don girmama Barmani, mun zanta da ita ta yi bayani na rayuwarta da yadda ta shiga waƙa da yadda ta samu suna CHOGE da sadaukar da kanta ga addinin musulunci. ‘Yan karyar Hausa zalla na duniya kakaf su fito da abu ɗaya tak da su ka yi na mutuntawa ko girmama rayuwar Barmani a lokacin da ta ke raye har ta ji dadi da har su ke da hurumin amfani da sunanta wajen zagin Nana Asma’u. Mu na jira daga nan zuwa mako daya in Allah ya ara ma na tsawon rai.
Duk wanda ya zama mai halin Fir’auna musamman da ya daura yin yaƙi da Allah zai gane shi makaskancin makaskanta ne. Ai har Fir’auna ya taba cewa Wazirinsa Hamana ya shirya ma sa tsani da zai hau sama don artabu da Allan Annabi Musa. A karshe wa kogi ya hadiye?. Mu’ujizar da Allah ya yi wa Annabi Musa AS ya bugi ruwa da sandarsa ya dare gida biyu hanya shararra ta bayyana jama’arsa ta tsira, haka Allah kan azurta bayinsa na gari da dacewa in da addu’arsu ke samun karbuwa. Manyan bayin Allah a tarihin Musulunci sun yi ayyuka masu ban al’ajabi na bunƙasa kiran Musulmi a ƙasashe masu ƙarfi kuma su ka yi galaba da taimakon Allah. Ba yawan rundunar musulmi ke kawo nasara ba, a’a yakini da sallamawa ikon Allah. A yaƙin Badar ai Allah ya turo rundunarsa ta taimakawa Musulmi su ka yi galaba kan gagarumar rundunar Mushurkai. Koyaushe Mushurkai na tsammanin karfin mamaki ko girman runduna ne kan ba su nasara. Duk rundunar da ba Allah a tafiyarta za ta sha kasa kuma ko da a wani lokaci ta na ganin ta na ganin ganiyar ƙarfi da iya kulle-kulle na makirci.
Tamkar yadda Allah bai karbi tuban Fir’auna ba don sai da ya ga mutuwa ya miƙa wuya, da alamu ‘yan bazata sai sun ga rundunar Allah za su nemi yin nadama amma bakin alƙalami ya bushe.
“Tsaunin kumfa taron banza dan yayyafi ka watsawa”
Na tabbata ɗimbin Musulmi da ke gudanar da hajjin bana kuma su ka taru a filin arfa da kuma waɗanda ke gida su ka samu yin azumin mai falala na arfa, sun ga sakon nan don yin addu’a ta musamman ta neman Allah SWT ya tarwatsa makircin ‘yan bazata a fadin duniya da kuma masu yi wa yankin Arewa zagon ƙasa ta hanyar ruruta fitinaar ƙabilanci tsakanin musulmi.
Ranar arfa ta kasance mafi samun karɓuwar addu’a daga Allah SWT don haka duk masu tauhidi sun dage sun yi wannan addu’ar kuma in Allah ya yarda a dan kankanin lokaci za a ga sakamakon aduu’ar inda ‘yan bazata za su yabawa aya zaƙi.
Hakika ‘yan bazata sun duƙufa haiƙan sai sun hargitsa salama tsakanin musulmi don yadda su ke da tsananin ƙiyayyar addinin Musulunci a zuciyarsu. Mun tabbata yankin Arewacin Nijeriya na riko sau da kafa da addinin Musulunci, don haka ya ke jerin sassan da ‘yan bazata ke marmarin kyastawa ashana.
Allah mun gode ma ka da ka ba mu ikon gudanar da wannan addu’a don mu na da yakini Allah ba zai bar masu yi wa tarihin Manzon Allah SAW sharri ba su cigaba da dabdala ba. Ko yanzu sai jifan juna su ke yi da miyagun kalamai.
KAMMALAWA
Mu na ƙara godiya ga Allah SWT da ya azurta wannan yankin na mu da Shehu Mujaddadi wanda ya yi aiki tuƙuru don ƙarfafa koyarwar musulunci ba tsumbure. Tasirin aikin Shehu da ya hana hatta turawan mulkin mallaka iya cin karesnsu ba babbaka ke zama abin haushi da cizon yatsa da ‘yan bazata ke ɓullo da duk dabaru na makarkashiya don aibantawa da muzantawa ga wannan aiki na Allah.
