Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi
Adadin ma’aurata 300 ne, watau angwaye da amare 600, za a ɗaura wa aure karo na uku na auren gatan da gwamnatin Jihar Kebbi ta ɗauki nauyinsa.
Matar Gwamnan Jihar, Nafisa Nasir Idris, ta ɓullo da wannan tsarin na auren gata a ƙarƙashin asusunta na NANAS Foundation, wanda Gwamna Nasir Idris ke bai wa cikakken goyon baya da taimakon kuɗaɗe da kuma kayayyakin alatu na ɗakunan amare.
Da yake ma manema labari bayani ranar Talata a Birnin Kebbi, shugaban babban kwamiti na auren gatan, tsohon mataimakin gwamnar Jihar Kebbi, Alhaji Suleiman Muhammad Argungu, Jarman Kabi, yace, gwamnati ta ɗauki nauyin biyan kuɗin Sadaki Naira miliyan 75, na ma’auratan gaba ɗayansu.
Ya ce gwamnati za ta biya Naira 250,000 a matsayin Sadaki na kowace amarya na ma’auratan 300, sannan kuma, za ta basu gadaje da katifu da zannuwan gado da kayayyakin aikin gida da kuma abincin dafawa.
Jarman Kabi yayi bayanin cewar wannan shine karo na uku da gwamnatin Jihar Kebbi ke shirya auren gata, wanda a wannan karon, waɗanda akayi ma gata sune, ‘yan mata marayu da suka kai munzalin aure, da matan da mazajensu suka rasu da kuma jawarawa.
Ya ƙara da cewar dukan amaren an basu damar su zabi mazajen da ransu ke so daga mazaɓu 225 da ke ƙananan hukumomi 21 da ke Jihar Kebbi.
Shugaban kwamitin yace a matsayin Jihar Kebbi mai mabiya addini daban-daban, gwamnati tana marhabin da mabiya addinin Islama da kuma na Kiristanci su shiga cikin auren gatan, idan sun cika sharuɗan da aka gindaya, yana mai cewar, a bara, wasu kiristoci sun shiga cikin auren gatan.
Ya ce sharuɗan sun haɗa da duk mazajen da za’a ɗaura ma aure, suna da sana’ar yi, da kuma ɗakin da za’a kai amarya, gidan miji nashi na kanshi, ko kuma gidan haya, sannan kuma za’ayi gwajin jinin ma’aurata domin tabbatar da cewar sun dace da juna, (DNA Test).
Jarman Kabi yayi bayanin cewar duk masu ruwa da tsaki a wannan harkar, sunyi ittifakin cewar a gudanarda ɗaurin auren a ranar 27 ga wannan watan Yuli, 2026.
