Tare da BILKISU YUSUF ALI, Ph’D
Gabatarwa
Kiwon dabbobi yana da muhimmanci ƙwarai da gaske kuma ana iya yin sa a wajen da ya dace a ko’ina amma rashin tsafta yana haifar da wari da cututtuka musamman lokacin damina. Don haka duk wanda yake kiwon dabbobi yana ruɓanya ƙoƙarinsa na tsafta ne don samun muhallin kiwo mai tsafta wanda ba zai cutar da kansa ba sannan ya cutar da makwabtansa ba da ma su dabbobin kansu.
Ma’anar wurin kiwo
Wurin kiwo shi ne wurin da ake renon dabbobi. Ya kamata ya kasance mai tsafta a bushe, da magudanar ruwa. Sannan ya kamata ya kasance akwai inda iska za ta fita ta kewaya kuma ana neman shawarwarin likitoci don a samu wani sinadari da za a ke amfani da shi don kasha wari kuma wanda ba zai cutar da dabbobin da masu kiwon ba. Wurin kiwo yana iya zama a buɗe ko a rufe, a cikin gida ko wani wuri na musamman da aka tanada ton kiwon.
Abubuwan da ke haddasa wari
Taruwar abubuwa da yawa kuma da rashin kula shi ke janyo wari a wurin kiwo wanda zai cutar da dabbobi ya cutar da mai kiwo sannan ya cutar da makwabta. Daga ciki akwai taruwar kashin dabbobi ba tare da an kwashe ba da fitsarin dabbobin da rashin magudanar ruwa da ragowar abincin da rashin iska a wasu lokutanma musamman ga masu kiwon kaji sukan bar su a nan bayan an samu matattu.Wanda wannan duka ana iya shawo kansu in har an bi dokar kiwo musamman abin da ya shafi tsafta.
Illar damina ga dabbobi da ba su samu kulawa ba
Abubuwa da dama kan kawo illa ga kiwo musamman a lokacin damuna. Daga ciki akwai taruwar ruwa da laka da yawaitar ƙwari da gurɓatar muhalli da yaɗuwar ƙwayoyin cuta. Haka rashin wadatacciyar iska shi ma yana kawo illa da damuna ga dabbobi.
Hanyoyin gargajiya
Akwai abubuwa da dama da masu kiwo ya kamata su yi amfani da su a gargajiyance wanda za su taimaka wa wurin masu kiwo don kariyar lafiya da muhalli da samun albarkar kiwo. A gargajiyance ana son amfani da toka da tono magudanar ruwa da amfani da ganyen darbejiya da yawan kwashe shara, busar da wuri. A tabbatar da ruwa ba ya kwanciya an kuma samar da hanyar ruwa.
Hanyoyin zamani
Akwai hanyoyin da ake bi a zamanance don ganin an tsaftace wurin kiwo ba tare da ya cutar da masu kiwo da dabbobin ba. Don tabbatar da ire-iren waɗannan magunguna yana da kyau a nemi shawarar likitocin dabbobi da kuma magani na kawar da cutoci da na kawar da wari. Sannan ana iya amfani da Disinfectant, composting, lime, isasshen iska, tsarin zubar da shara, tsaftace kullum.Disinfectant, composting, lime, isasshen iska, tsarin zubar da shara, tsaftace.
Illar da rashin tsaftar muhallin kiwo yake yi wa lafiyar ɗan’adam
Akwai illa da rashin tsafta yake janyo wa waɗanda ke mu’amala da dabbobin kamar masu kiwo ko masu mu’amala da su ko kuma makwabtansu. Misali Gudawa da kwalara da taifod da cututtukan fata da matsalar numfashi.
Illar da rashin tsaftar muhallin kiwo yake yi wa lafiyar dabbobi
Haka su ma dabbobin in wurinsu ba tsafta ba za su ke girma ba za su ke gudawa ba za su bayar da nono yadda ya kamata in masu bayar da nono ne haka kuma za su ke yawan rashin lafiya da za ta ma iya kai wag a rasa dabba.
Shawarwari
A tsaftace kullum, a samar da magudanar ruwa, horas da masu kiwo, a ke tuntuɓar binciken likitocin dabbobi. Tsaftar wurin kiwo na kare lafiyar jama’a da dabbobi kuma yana rage asarar tattalin arziki. Duk lokacin da aka ga wani abu sabo a tuntuɓi likita don shawo kan matsala. Kamar ɗan’adam su ma dabbobi suna buƙatar kulawa ta musaamman don samunsu masu lafiya da fatan samun albarkarsu ta hanyar kiwo. Haka mutane da suke mu’amala da su yau da gobe suma su samu damar kuɓuta daga cutarwar da rashin tsaftar zai iya haifarwa.
