Kano: Da lafiya ilimi ke wanzuwa – Masanin lafiya a Bichi

Spread the love

Bisa la’akari da abubuwan da suke haddasa Cutar Tetanos da ake rasa rayuwar ‘ya’ya mata, musamman masu juna-biyu da ake yin biyu babu wajen mutuwar uwa da ɗa a yayin naƙuda, sakamakon shigar cutar ta hanyar jin ciwo ko rauni.

Jami’ar Yaɗa Labarai ta Ƙaramar Hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta rawaito, Jami’in Kula da Harkar Sadarwa da Wawala na Sashen Lafiya dake Bichi, Malam Nura Ibrahim Abubakar, ya gudanar da zama na musamman tare da Sashen Hukumar Iimi na yankin haɗi da Ƙungiyar Malamai waɗanda suka shafi ɓangaren makarantun mata a ƙaramar hukumar.

Bayan ɗimbun godiya da ya yi ga Hukumar Ilimin yankin bisa namijin ƙoƙarin da take yi game da gudanar da allurar rigakafi a makarantun na mata, ya ce:

“Kiwon Lafiya harka ce ta al’umma baki ɗaya ba iya mu kaɗai ba. Don haka muna ƙara neman haɗin kan Hukumar Ilimi domin ilimi shi ne ɗan’adam kuma tushen komai, lafiya kuma uwar jiki ce tilas sai da ita ilimi da komai yake wanzuwa.

Duba da wannan ya sa muke ƙara neman ƙarin taimakonsu a dukkan al’amuranmu, domin mu samu mu daƙile cututtukan nan da ake ta ƙoƙarin yadda za a yaƙe su; rigakafi ya fi magani kuma shi ne bayar da shi kyauta, idan ciwo ya kama mutum kuma sai ya sayi magani!” Malam Nura Ibrahim Abubakar.

Shi kuwa Sakataren Ilimi na yankin, Alhaji Bashir Ishaq Muhammad, cewa ya yi hakan yana daga manufar sake fahimtar da malaman makaranta, mahimmancin wannan rigakafin, ta yadda za su wayar da kan ɗalibai mata da iyayensu, daga bisani kuma ya nuna matuƙar jin daɗi bisa wannan gagarumin aiki na haɗa ƙarfi da ƙarfe a tsakanin Sashen Lafiya da Hukumar Ilimin yankin suke yi a kodayaushe domin cim ma nasarar aikin.

“Muna godiya sosai matuƙa ga jami’an lafiya, domin waɗannan allurai ba na cutarwa ba ne, suna ba da kariya ne ga lafiyar yara da matasa da ƙanana. Haka kuma muna jinjina ga Shugaban ƙaramar hukuma bisa jajircewarsa na duk abin da zai kawo wa ƙaramar hukumarmu cigaba.” Alhaji Bashir Ishaq.

Da yake jawabi, Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Makarantun Sakandari na yankin, Malam Ibrahim Ahmed Bichi, ya ce, a shirye suke wajen ci gaba da ba da haɗin kai a duk sadda za a gudanar da allurar rigakafi irin wannan ga lafiyar al’umma bisa mahimmancinta, kuma suna godiya da fatan alheri.

A nata ɓangaren Shugabar Ƙungiyar Mata dake ƙarƙashin Sakataren Ilimi a Hukumar Ilimin, Malama Asma’u Jume Ahmad, sun ƙudiri aniyar bi gida-gida wayar da kan al’umma mahimmancin wannan rigakafin ƙarƙashin jagorancin Sakataren Ilimin.

“Mu mata ne; mun san illar wannan cutar, mun ga waɗanda suka mutu ba ƙarya ba ne, amma sakamakon cigaba da ake ta samu a yanzu ga shi an samar mana rigakafin da za a daƙile wannan cutar, kuma duk wadda aka yi mata rigakafi daga ƙarancin shekarun da ake fara yinta sai ta fi amfana da rigakafin fiye da wadda ta yi bayan aure.” Malama Asma’u Jume Ahmad.

By Babaji

Leave a Reply