
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jagoran marasa rinjaye na Majalisar Wakilai ta tarayya, Kingsley Chinda, ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC, sannan ya yi murabus daga muƙaminsa na shugaban marasa rinjaye.
Kakakin Majalisar Wakilai ya karanta wasiƙar sauya sheƙarsa a zaman majalisar na ranar Talata. Chinda, wanda ke da kusanci da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya samu tikitin takarar gwamnan APC a Jihar Rivers domin zaɓen 2027.
Haka kuma, wasu ’yan majalisar da dama sun sauya jam’iyya. ’Yan majalisar shida daga Jihar Oyo sun fice daga PDP zuwa jam’iyyar APM, yayin da ɗan majalisa daga Jihar Bauchi, Auwalu Abdu Gwalabe, shi ma ya koma APM.
