Tinubu ya jagoranci gwamnoni, Abdul Samad BUA da wasu a liyafar Saudiyya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abujal

A ranar Lahadi Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci wasu gwamnoni da mambobin tawagarsa Makkah, Saudiyya domin liyafar cin abincin dare tare.

Gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara, Mai Mala Buni na Yobe, Babagana Zulum na Borno, Uba Sanin Kaduna da Ahmed Aliyun Sakkwato.

Sauran manyan jami’an gwamnati da ke wajen sune: Antoni Janar na Ƙasa (AGF) kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi; Mai ba wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa, Ibrahim Masari; Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu; da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Haka kuma akwai Attajiri Abdul Samad Rabiu, Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA, wanda shi ma ya samu halartar taron. A yayin haka, Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya mayar da bambance-bambancen sa ke tsakanin ‘yan Nijeriya zuwa nasarori domin ci-gaban ƙasar.

A nasa jawabin Abdul Samad BUA ya ce, zuwansu Makkah wata dama ce ta yi wa Nijeriya addu’o’in samun nasarori. Ya bayyana cewa tawagar Nijeriyar tana godiya bisa samun damar yin addu’o’i ga kawunansu, iyalansu da ma Nijeriya a matsayinta na ƙasa, yana mai cewa wannan shi ne karo na uku da shugaban yake gayyatar su zuwa liyafar cin abinci tun isarsu Saudiyya.

Da yake jawabi a madadin gwamnoni, Gwamna AbdulRazaq ya yi addu’ar Allah ya ba wa Shugaban Nijeriyar ƙarfi, hikima da ƙwarin-gwiwar jagorantar ƙasar. Shi Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin Soshiyal Mediya, Dada Olusegun ya wallafa cewa, Tinubu ya gayyaci manyan ‘yan Nijeriyar ne domin tattauna wasu muhimman batutuwan da suka shafi ci-gaban ƙasa.

By Babaji

Leave a Reply