Gidauniyar Gwagware ta yi Allah wadai da hare-haren da aka kai wa ayarin motocin APC a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gidauniyar Musa Adamu Gwagware tayi tir da Allah wadai da hare haren da aka kai ma motocin ayarin ya’yan jama’ar APC waɗanda suka fara yaƙin neman zaɓen 2027 a shiyar Funtua.

Shugaban Gidauniyar Kwamred Mannir Suleiman ya bayyana haka a watar sanarwar da ya fitar ɗauke da sanya hannun sa bayan da wasu matasa suka sake kai hare hare ga ayarin matocin su a garin Yankara kan hanyar su ta zuwa Funtua.

Kwamred Mannir Suleiman yace wannan babban bala’i ne da idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba zai yi munin da nan gaba ba duk wata hidima na siyasa zai gagara a Jihar.

Ya yabawa jami’an ‘yan sanda kan matakan da suka ɗauka a garin Malumfashi bayan da lamarin ya faru,ya yi fatan za su ɗauki irin wannan mataki na gano da kama waɗanda suke aiwatar da wannan ta’adanci ” Ba ma kama waɗanda suka aikata wannan ta’adanci a gano waɗanda suka ɗauki nauyin ta’adancin.

Shugaban Gidauniyar ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar APC a Jihar Katsina da su kai hankali nesa su bar jami’an tsaro su yi aikinsu kada su ɗauki doka a hannun, ya yabawa ya’yan jam’iyyar bisa irin dattaku Da sanin yakamata wajan ganin basu kula ba.

Ya kuma yaba wa jami’an tsaro kan matakan da suka ɗauka a Malumfashi wanda daƙile tare da kama wanɗanda ake zargi da kitsa wannan ta’adanci.

Kwamred Mannir ya yi kira ga jami’an tsaro da su ɗau mataki irin wanda suka ɗauka a garin Malumfashi da zaƙulo waɗanda suka aikata wannan ta’adanci dama masu ɗaukar nauyin su.

Ya jinjina wa al’ummar Funtua da sauran ƙananan hukumomi na shiyar bisa karamci da ƙaunar da suka nunawa Gwamna Dikko Raɗɗa a yayin da ya kai ziyara a yankin.

Ya ja hankalin matasa a yankin da ma jiha baki ɗaya da su guji duk wani abinda zai kawo matsalar tsaro a faɗin jihar.

By ukarofi

Leave a Reply