Kano 2027: Umarnin kotu ne silar cire sunan Abdulsalam Gwarzo, inji INEC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta bayyana cewa ba ta da wata matsala dangane da takarar ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NDC, Abdussalam Gwarzo, inda ta ce wani unarnin kotu ne ya sa ba a ga sunansa ba a jaddawalin ‘yan takarar da ta sabunta na zaɓukan 2027.

INEC ta ce ta riga ta tantance Gwarzo bayan nazari kan ƙorafe-ƙorafen da take da su kan cire sunayen ‘yan takara bayan fitar da jaddawalin farko a ranar 10 ga Oktoba, 2026, amma ta ce ba za ta wallafa sunansa ba sai Babbar Kotun Jihar Kano ta yi hukunci kan umarnin a ranar 27 ga Oktoba.

Wani babban jami’in INEC, wanda ya gana da wakilinmu, ya ce hukumar ba ta da wata matsala da takarar ɗan NDCn, inda ya bayyana cewa takunkumin kotu ne kaɗai matsalar da sa ba saka sunansa ba sabon jaddawalin ‘yan takarar. Wanna ya biyo bayan binciken da jaridar Daily Trust ta yi a ranar Asabar, inda ta gano cewa babu sunan Gwarzo da abokin tafiyarsa, Rabi’u Mustapha acikin jaddawalin da INEC ɗin ta sabunta.

Tun a ranar 10 ga Oktoba ne dai Abdussalam Gwarzo ya yi wa INEC ƙorafin cewa bai ga sunansa ba cikin jaddawalin da aka fitar a ranar 10 ga Oktoba. Da fari, Mohammed Haruna, wanda kwamishinan ƙasa ne na hukumar ya bayyana cewa an ɗauki ƙorafin Gwarzo a matsayin wanda ya yi nasara, saidai za a wallafa sunansa ne bayan fitar da sakamakon hukuncin Babbar Kotun Tarayya ta jihar Kano kan umarnin gaggawa da ta bayar game da matsalar.

A ranar 27 ga Oktoba ne NDC ta garzaya Babbar Kotun Tarayya ta Abuja domin shigar da ƙorafin rashin ganin sunan ɗan takararta a jaddawalin ‘yan takarar gwamna da hukumar zaɓen ta fitar. A ciki ta nemi kotun ta umarci INEC ta sanya sunansa a jaddawalin.

Wasu rahotanni a ranar 29 ga Oktoba sun nuna cewa INEC ta amince da ƙorafin Gwarzo tare da na tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami na Jihar Gombe da na wasu ‘yan takara da da fari ba su ga sunayensu ba. Saidai ta ce ta yi haka ne bisa sakamakon da shari’o’in da ke kotuna za su nuna kan hukuncin nata.

By Babaji

Leave a Reply