An soke wasu kayan aure tare da ƙayyade kuɗin baiko zuwa N50,000 a Charanchi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sarkin Shanun Katsina Hakimin Charanchi, ya bayar da umarnin soke wasu daga cikin kayan da ake buƙata yayin hidimar aure a gundumar Charanchi ta Jihar Katsina.

A wata “takardar gabatar da dokar soke kayan baiko da kayan ƙorai na uwar miji da uban miji a gundumar Charanchi”, Hakimin ya ce matakin ya biyo bayan la’akari da shawarwari da koke-koken da matasa da iyayen ‘ya’ya mata daga yankin suka gabatar masa.

Ya bayyana cewa koke-koken sun shafi yadda wasu abubuwan da ake buƙata yayin hidimar aure suka wuce ƙima, lamarin da ke ƙara wa al’umma nauyi.

Saboda haka, ya bayar da umarnin cewa daga yanzu kayan baiko an soke tsarin da ake bi a baya, inda aka maida kayan baikon zuwa Naira N50,000 da tiyar dabino ɗaya zuwa biyu. An soke bayar da kayan ƙorai ga uban miji da kayan ƙorai ga uwar miji shima haka.

Hakimin ya ce an ɗauki matakin ne bisa la’akari da yanayin da al’umma ke ciki, yana mai cewa wasu daga cikin waɗannan abubuwa ba su da tushe a Musulunci.

Ya kuma gargaɗi duk wanda aka samu yana ƙarya wannan doka cewa za a ɗauki matakin hukunci a kansa.

Daga ƙarshe, Sarkin Shanun Katsina ya yi kira ga al’ummar Gundumar Charanchi da su kiyaye umarnin, tare da addu’ar Allah ya ba su lafiya da zaman lafiya.

By ukarofi

Leave a Reply