‘Allah ke bada mulki da karɓewa’: Saƙon Tinubu ga ‘yan Nijeriya yayin da ya shiga Ka’abah

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce Allah ke da cikakken iko da mulki, wanda ka iya karɓewa daga wane ya bai wa wane. Tinubu ya faɗi haka ne a lokacin da ya ziyarci Ɗakin Ka’abah a Makkah, inda ya ce ya yi addu’ar neman hikima da jajircewa wajen sauke nauyin da aka dora musu na yi wa ‘yan Nijeriya hidima.

Shugaban ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin bayan kammala aikin Umara a Saudiyya, kamar yadda Kakakinsa Bayo Onanuga ya bayyana a wata sanarwa. Da yake magana kan nauye-nauyen da ke cikin riƙe muƙamin gwamnati, Tinubu ya ce dukkan wanda aka ɗora wa nauyin jagorantar al’umma, wajibi ne ya sauke bisa ƙwarewa, yana mai cewa mulki na Allah ne.

“Babu wani abin bauta sai Allah. Shi ne mai bayarwa kuma mai karɓa. Shi ke da mulki da iko,” inji shi.

Shugaban ya kuma miƙa godiyarsa mara adadi ga Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud da kuma Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman bisa ba shi da dama tare da ‘yan tawagarsa ta shiga cikin ɗakin Ka’abah, yana mai bayyana hakan a matsayin abin da zai shiga cikin kundin tarihi.

Kazalika, Shugaban ya jaddada aniyarsa ta cigaba da hidimta wa Nijeriya, inda ya ce zai cigaba da fafutukar nasarori da ci-gaba mai ɗorewa ga ƙasar, yana mai cewa halin matsin tattali da al’umma suka tsinci kansu a ciki ba zai tafi kara zube ba.

‘Yan tawagar shugaban Nijeriyar sun haɗa da Antoni Janar na Ƙasa (AGF), Lateef Fagbemi; Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma, Farfesa Ali Pate; gwamnonin jihohin Borno, Sakkwato, Jigawa, Kaduna, Yobe da Kwara; da kuma jagororin ‘yan kasuwa Abdul Samad Rabiu BUA da Wale Tinubu.

By Babaji

Leave a Reply