TMG: Abin da ya sa APC ba za ta takura wa gangamin ‘yan adawa ba – Yilwatda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki da Gwamnatin Tarayya za su cigaba da sakar wa ‘yan adawa mara domin su yaɗa manufofinsu saboda hakan wani ɓangare ne mai muhimmanci a tsarin dimukraɗiyya.

Yilwatda ya yi wannan bayani ne yayin karɓar baƙuncin kwamitin binciken ƙwaf kan lamuran gabanin zaɓe na Ƙungiyar Ƙasashen Afirka ta Yamma Masu Ƙarfin Tattalin Arziƙi (ECOWAS), ƙarƙashin jagorancin tsohon Maitaimakin Shugaban Ƙasar Sierra Leon, Mai Girma Victor Bockarie Foh.

Farfesan ya bayyana cewa wajibi ne a bar ‘yan ƙasa da ‘yan adawa su riƙa bayyana ra’ayoyinsu ba tare da kame, wulaƙantawa ko dukkan wani nau’i na takura musu ba. Ya ce, ya dace a samu jam’iyya mai mulki mai ƙarfi tana da ƙwarin-gwiwar yin siyasa a ƙarƙashin dokokin dimukraɗiyya yayin ƙoƙarin bayar da kariya ga ɓangarorin adawa wajen bayyana ra’ayoyinsu.

“Kasancewar jam’iyyarmu ce mafi girma ba ya nufin mu na son yin danniya ga kowaye. Mu na son fagen dimukraɗiyyar da zai zama kowace jam’iyya za ta iya shiryawa, gudanar da yaƙin neman zaɓe da neman goyon bayan ‘yan Nijeriya ba tare da tsoro ba,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, jam’iyyar APC ta fahimci yadda ake gasa a tsarin dimukraɗiyya duba da cewa ta fuskanci matsalolin faɗuwa zaɓe a baya. Ya bayyana cewa, jam’iyyar a ire-iren waɗannan halaye ta dama da masu ruwa da tsaki ta nemi haɗin kai da abokan tafiyarta, inda ya bayar da misali da faɗuwa a zaɓukan gwamnonin Anambara da Osun da APC ta yi.

A cewarsa, tsare-tsare da dabarun gudanarwar APC ya taimaka mata wajen yin fintinkau cikin sauran jam’iyyun siyasar Nijeriya. Ya ce, baya ga nasarori, ƙarfinsu ya ginu ne akan adadin mabiya, tsare-tsare daga tushe, wakilcin masu riƙe da muƙaman zaɓe, ƙungiyoyin goyon baya a faɗin ƙasa da dai sauransu.

Kazalika, Shugaban APCn ya ce jam’iyyar tana da jimillar rajistar mambobi miliyan 13 a baki ɗaya sassan ƙananan hukumomin Nijeriya, waɗanda aka tantance su ta lambobin katin ɗan ƙasa (NIN) da bayanan masu zaɓe. Har ila yau, Yilwatda ya ce APC tana da zaɓaɓɓun mambobi sama da guda 261,000 a matakai daban-daban, wanda ke nuna ƙarfinta a siyasance a Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply