
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun tsaro ƙarƙashin Atisayen Haɗin Kai da ke Arewa maso Gabas, ta yi nasarar halaka mayaƙan ƙungiyar ISWAP da dama, ciki har da wani mamban kwamitin shura mai suna Abu Hajara da wani sanannen kwamanda, Abul Walid yayin wata ba-takashi a yankin Kukawa da ke Jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa, an kuma halaka wasu manyan mayaƙa Larabawa biyu yayin arangamar, wadda ta gudana a ranar 31 ga Oktoba, 2026. Abul Walid ya shahara a matsayin babban na hannun daman Ba Shuwa, wato babban Walin ISWAP.
Jami’in hulɗa da jama’a na riƙo na rundunar soji a Arewa maso Gabas, Kyaftin Mohammed Goni ne ya bayar da labarin a wata takarda da ya fitar ranar Lahadi, 1 ga Nuwamba, 2026. A cewar saƙon takardar, dakarun tsaron da aka tura aiki a Kukawa sun yi nasarar daƙile wani babban harin ISWAP a sansanoninsu, inda sojojin ƙasa suka samu agajin na sama na Atisayen Haɗin Kai.
Bayan wannan musayar wuta, dakarun tsaron sun kuma ƙwato waɗansu muggan makamai, harsasai da na’urorin sadarwa. Rundunar ta bayyana atisayen a matsayin ishara ga ƙoƙarin sojojin wajen zama cikin shiri da ƙarfin mayar da martani akan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a sassan shiyyar.
Wannan hari akan dakarun na Kukawa na zuwa ne ƙasa da kwana uku bayan ɓarin wuta tsakanin sojoji da ‘yan ta’adda a Buni Yadin Jihar Yobe, inda aka halaka ‘yan ta’adda 55, a cewar soji. Daga cikin waɗanda aka halaka a akwai kwamandoji kamar Ali Mandara Abba Gajiri da aka sani da Munzir; Habu Ikkima Nakif Yana Faruk; da kuma Kwamanda Gogore.
A ƙarshe, rundunar ta jaddada aniyarta ta ƙoƙarin cigaba da bai wa fararen hula masu biyayya ga dokokin ƙasa kariya da cigaba da ƙaddamar da hare-hare akan ‘yan ta’adda da lalata sansanoninsu a shiyyar.
