Ina ƙarama sosai kakata ta yi min kaciya — Ayodeji Bello-Awodoyin

Spread the love

“Ba zan bar Jihar Osun yadda na same ta ba”

Daga AISHA ASAS

Mai karatu, barkanmu da sake kasancewa da ku a shafin Gimbiya na jaridarku ta Blueprint Manhaja, inda muke haska rayuwar mata, mu waiwayi tafiyarsu, mu kalli ƙalubalen da suka fuskanta, mu kuma nazarci darussan da za a iya ɗauka daga abubuwan da suka faru da su. Domin a rayuwa, ba nasara kaɗai ce ke ba da labarin mutum ba; a wasu lokuta, yadda mutum ya fuskanci ƙalubale da kuma yadda ya bi hanyoyin da suka dace wajen warware su kan bayyana wasu muhimman ɓangarori na rayuwarsa.

A wannan makon, za mu dubi rayuwar Ayodeji Bello-Awodoyin, wata ’yar Najeriya da ta mayar da gwagwarmayar kare ’yan mata daga kaciya wani muhimmin ɓangare na rayuwarta. Abin da ya sa tarihinta ya bambanta shi ne yadda ita kanta ta fuskanci wannan al’ada tun tana ƙarama, amma daga baya ta zaɓi shiga sahun waɗanda ke ƙoƙarin kawo ƙarshenta.

A hirar da ta yi da jaridar The Guardian Nigeria, wadda Ijeoma Thomas-Odia ta rubuta aka wallafa ranar 11 ga Oktoba, 2025, Ayodeji ta bayyana cewa kakarta ce ta yi mata kaciya tun tana ƙarama, saboda a lokacin ana kallon hakan a matsayin abin da al’ada ta tanada. Ta kuma bayyana cewa ƙwarewar da ta samu a rayuwarta ta taimaka wajen ƙarfafa mata gwiwar shiga fafutukar kare haƙƙin mata da ’yan mata.

Sai dai abin da ya fi jan hankali a tarihinta ba wai abin da ya faru da ita kaɗai ba ne. Yadda ta tashi daga matsayinta na ɗaliba zuwa mai wayar da kan al’umma, yadda ta fara gudanar da ayyuka da kuɗin aljihunta, da kuma yadda ta shiga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa masu yaƙi da kaciya, duk suna daga cikin abubuwan da suka sanya tarihinta ya cancanci kulawar mai karatu.

Ta yaya kaciya da aka yi mata tun tana ƙarama ta zama farkon wata tafiya ta kare sauran ’yan mata?

A cewar Ayodeji, abin da ya faru da ita tun tana ƙarama ya kasance wani ɓangare na dalilan da suka sa ta shiga fafutukar kawo ƙarshen kaciya. Ta bayyana cewa ba wai sha’awar kare haƙƙin ɗan Adam da kawo sauyi a cikin al’umma ne kawai suka ja hankalinta ba, har da abin da ta fuskanta a rayuwarta.

Wannan batu yana da muhimmanci wajen fahimtar tafiyarta. Domin akwai bambanci tsakanin wanda ya karanta game da matsala a littafi da wanda ya san cewa matsalar tana iya shafar rayuwar mutum tun kafin ya kai shekarun da zai iya fahimtar abin da ake yi masa.

Saidai ba kowane mutum ne yake mayar da abin da ya faru da shi zuwa wata manufa ta taimaka wa wasu ba. Ayodeji ta zaɓi yin amfani da ƙwarewarta wajen wayar da kan jama’a, domin ta taimaka wajen ganin sauran ’yan mata ba su shiga irin wannan yanayi ba.

A nan ne za mu fahimci ma’anar kalmar da ta ambata a firar ta cewa ba za ta bar Jihar Osun yadda ta same ta ba. Wannan ba furuci ne kawai na nuna ƙuduri ba; a cewar bayanan da ta bayar, ya zama wani ɓangare na aikin da ta fara tun tana jami’a, lokacin da ta fahimci cewa akwai buƙatar a yi magana kan kaciya da illolinta.

Wane mataki ta fara ɗauka domin ganin an kawo sauyi?

Ayodeji ta karanci ilimin zamantakewa da nazarin al’umma, wato Sociology and Anthropology, a Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, Jihar Osun.

A lokacin karatunta, ta fahimci girman matsalar kaciya a jihar, musamman bayan ta gano cewa bayanan binciken lafiyar jama’a na Najeriya na shekarar 2018 sun nuna yawan kaciya a Osun ya kai kashi 76 cikin 100 a tsakanin mata masu shekaru 15 zuwa 49 da aka bincika.

Wannan bayani ya ƙara ƙarfafa mata gwiwar ɗaukar mataki. A maimakon ta jira sai ta kammala karatu ko ta samu wani babban matsayi, ta fara da abin da take da shi a lokacin.

Ta fara shirya tattaunawa a ɗakin kwanan ɗalibai, inda take wayar da kan takwarorinta game da kaciya da dalilan da ya sa ya dace a sake nazarin wannan al’ada. Daga baya, ta nemi kujerar mataimakiyar shugabar ƙungiyar ɗaliban da ke karantar ilimin zamantakewa da nazarin al’umma, ta samu nasara, sannan ta yi amfani da damar wajen faɗaɗa ayyukan wayar da kai a jami’ar.

Wannan mataki ya nuna yadda ta fara gina tafiyarta tun daga ƙaramar al’umma da take ciki. Ba ta fara da shirye-shiryen duniya ko tarukan manyan mutane ba. Ta fara ne da tattaunawa da mutanen da suke kusa da ita, tana ƙoƙarin ganin sun fahimci matsalar da kuma yadda za a iya magance ta.

Daga nan, ta faɗaɗa aikinta zuwa ƙauyuka da sauran al’ummomin Jihar Osun, inda ta bar yanayin jami’a da ta saba domin kai saƙonta ga mutanen da take ganin suna buƙatar jin saƙon.

Shin ta samu kuɗin gudanar da ayyukanta tun daga farko?

A’a, ba ta fara da wadataccen kuɗin gudanar da ayyuka ba. A hirarta, Ayodeji ta bayyana cewa ta yi amfani da kuɗin aljihunta wajen gudanar da wasu shirye-shiryen wayar da kai a farkon tafiyarta.

Wannan yana nuna irin ƙoƙarin da take yi wajen ganin an ci gaba da aikin duk da ƙarancin kuɗaɗe. Ta ci gaba da neman hanyoyin isar da saƙon nata, har daga baya wasu mutane suka fara ba ta tallafi, wanda ya taimaka wajen faɗaɗa ayyukan.

Da aka samu tallafin, ta bayyana cewa sun fara iya biyan kuɗin shirye-shiryen rediyo da talabijin, tare da wallafa bayanai a jaridu domin isar da saƙon ga jama’a da yawa.

Wannan ya taimaka wajen sauya yadda take gudanar da aikinta. A farkon tafiyarta, tattaunawa da ɗalibai da mutanen da ke kusa da ita ce babbar hanyar da take amfani da ita. Amma da samun tallafi, ta samu damar kai saƙon zuwa ga mutanen da ba za ta iya haɗuwa da su kai tsaye ba.

Duk da haka, ya kamata a fahimci cewa ƙoƙarin mutum ɗaya ba ya maye gurbin buƙatar samun isasshen tallafi. Masu fafutukar kare haƙƙin mata da ’yan mata suna buƙatar kuɗaɗe, horo da kayan aiki domin su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Wannan shi ne ɗaya daga cikin matsalolin da Ayodeji ta yi ƙoƙarin magancewa ta hanyar shiga ƙungiyoyin da ke tallafa wa masu aikin kai tsaye a cikin al’umma.

Me ya sa take ganin yaƙi da kaciya ya wuce magana kan al’ada kawai?

Kaciya ga ’yan mata, wadda ake kira Female Genital Mutilation (FGM) a Turanci, wata al’ada ce da ta ƙunshi yanke ko raunata al’aurar mace saboda dalilan da ba su da alaƙa da magani.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa wannan al’ada ba ta da wata fa’ida ta lafiya, kuma tana iya jawo matsaloli kamar zubar jini, kamuwa da cututtuka, matsalolin fitsari, matsaloli yayin haihuwa da kuma wasu illolin da kan daɗe suna shafar rayuwar wadda aka yi wa.

Duk da haka, ana ci gaba da yin ta a wasu al’ummomi saboda al’ada da aka gada, matsin lambar jama’a da kuma tunanin cewa tana daga cikin al’adun da ya kamata a kiyaye.

A irin wannan yanayi, masu fafutukar kawo ƙarshen kaciya suna fuskantar ƙalubale fiye da bayyana illar lafiyarta. Suna kuma buƙatar fahimtar dalilan da suka sa wasu iyalai ke ci gaba da yin ta, sannan su samar da hanyar da za ta taimaka wajen sauya wannan tunani.

Ayodeji ta fahimci cewa wayar da kai na daga cikin muhimman hanyoyin da za a bi wajen kawo sauyi. Idan iyaye suka fahimci illolin kaciya, suka kuma samu damar tattauna damuwarsu da ƙwararru da sauran mutanen da suka amince da su, za a iya taimaka musu su sake nazarin abin da suke ganin al’ada ce.

Wannan ba yana nufin a yi shiru kan illar da kaciya ke haifarwa ba ne. A’a, yana nufin a yi amfani da sahihan bayanan lafiya, ilimi da tattaunawa domin kare ’yan mata ba tare da mayar da wayar da kai zuwa cin mutuncin mutanen da ake son a taimaka musu ba.

Ta yaya ta samu damar kai saƙonta ga shugabannin al’umma?

Da farko, Ayodeji ta fara aiki ne a cikin jami’a. Amma daga baya ta faɗaɗa ayyukanta zuwa ƙauyuka da sauran al’ummomin Jihar Osun, inda ta yi ƙoƙarin tattaunawa da mutanen da ke da tasiri a cikin al’umma.

Rahoton da jaridar The Guardian ta Birtaniya ta wallafa a ranar 16 ga Fabrairu, 2022, ya bayyana yadda Ayodeji ta yi ƙoƙarin tattaunawa da shugabannin gargajiya kan kaciya. Rahoton ya nuna cewa a farkon ƙoƙarinta ta fuskanci rashin ɗaukar maganarta da muhimmanci saboda tana matashiya kuma ba ta yi aure ba.

Amma daga baya, wasu shugabannin gargajiyar sun fara tuntubarta domin tattauna batun kawo ƙarshen wannan al’ada.

Wannan wani muhimmin mataki ne a tafiyarta. A wasu al’ummomi, shekarun mace ko matsayinta na aure na iya shafar yadda ake kallon maganarta. Amma labarin Ayodeji yana nuna muhimmancin ci gaba da neman ilimi, gabatar da hujjoji da kuma gina tattaunawa da mutanen da za su iya taimakawa wajen kawo sauyi.

Haka kuma, ya nuna cewa ba za a iya magance matsalar da ta shafi al’umma ta hanyar magana da waɗanda suka riga suka amince da ita kawai ba. Ana buƙatar a shiga inda ake buƙatar bayani, a saurari damuwar jama’a, sannan a taimaka musu su fahimci yadda za su iya kare ’ya’yansu.

Ta yaya ta fita daga fafutukar jami’a zuwa matakin ƙasa da ƙasa?

Yayin da aikinta ke bunƙasa, Ayodeji ta samu damar shiga shirin Young African Leaders Initiatiɓe (YALI), wanda aka ƙaddamar a zamanin tsohon shugaban Amurka Barack Obama. A cewarta, wannan shiri ya taimaka mata wajen ƙara fahimtar jagoranci da gudanar da ayyukan al’umma.

Ta kuma samu horo daga Global Media Campaign Academy a Birtaniya, inda ta koyi dabarun yaɗa saƙonni da gudanar da kamfen kan kaciya.

A shekarar 2021, jaridar The Guardian Nigeria ta ruwaito cewa an naɗa ta mamba a kwamitin gudanarwa na Global Media Campaign, inda za ta wakilci matasa da matasa masu tasowa daga Afirka.

Ta kuma kafa ƙungiyar Initiatiɓe for Girls’ Rights and Health Development (IGRHD), wadda take amfani da hanyoyin yaɗa labarai, ilimantarwa, wayar da kai da tallafa wa waɗanda suka tsira daga munanan al’adu wajen ƙoƙarin kawo sauyi a cikin al’umma.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa

By ukarofi

Leave a Reply