
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Filato, ya zargi gwamnatin marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da siyar da ɗanyen man Nijeriya gabanin a haƙo shi, sannan yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu har yanzu tana biyan bashin da aka samar da wannan tsari. Mutfwang ya faɗi haka ne a ranar Litinin, yayin taron ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC don zaɓukan 2027 a gidan gwamnatin jihar da ke Rayfield a Jos.
Gwamnan ya zargi tsohuwar gwamnatin da alhakin ƙalubalen tattalin arziƙi da al’umma ta fuskanta, wanda Tinubu ya gada a 2023, inda ya kuma ce gwamnatin ta yanzu na buƙatar lokaci domin riskar da sakamakon gyare-gyaren da take yi ga ‘yan ƙasa. “Daga cikin matsalar gwamnatin Buhari, shi ne sun kai wani matsayi da ba su ma san mai za su yi ba, don haka suka siyar da ɗanyen manmu na nan gaba,” inji Mutfwang.
Ya ƙara da cewa, “Ɗanyen man da ba mu kai ga haƙowa ba daga ƙasa an siyar da shi kafin a karɓa. Kuma yau mu na biyan bashin. Don haka ba za mu yi tsammanin abubuwa su sauya cikin sauƙi nan take ba.”
Haka kuma, gwamnan Filaton ya bayyana halin tallafin fetur a gwamnatocin baya a matsayin badaƙalar ƙasa, inda ya ce gwamnatin ta karɓo rancen kuɗi domin biyan iƙirarin badaƙala da ya shafi wasu jami’an gwamnati. A cewarsa, cire tallafin fetur ya taimaka wajen samun wadatarsa duk da cewa farashinsa ya hauhawa sakamakon matsalolin da ake fuskanta a matakin duniya, yana mai cewa a baya an riƙa fuskantar dogon layin jiran siyan fetur inda a yanzu gwamnatin Tinubu ta warware wannan matsala.
Kazalika, ya bayar da kariya ga tsare-tsaren tattalin arziƙin gwamnatin Tinubu, inda ya yi iƙirarin cewa adadin kuɗaɗen ajiyar Nijeriya a ƙasashen waje ya haura Dala biliyan 50 daga matakin Dala biliyan 3 da ɗoriya da ta gada daga gwamnatin baya.
