
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Malaman addinin Musulunci daga ƙungiyoyi mabambanta da mambobin Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa (CAN), sun yi kira da a gaggauta yin adalci a fili a game da kisan Sheikh Ibrahim Yahaya Masussuka da wasu ‘yan bindiga suka aiwatar a makon da ya gabata.
Ɓangarorin sun yi wannan kira ne yayin suka taru a Jihar Katsina a taron haɗin kai da marigayin ya shirya. A cewarsu, yin adalci ne kaɗai zai hana aukuwar irin hare-haren da kashe-kashen malamai da masu wa’azi.
Ƙungiyar Ƙuraniyyoon da aka kira da ‘Yan Ƙur’ani Zalla ce ta shirya taron domin ƙarfafa haɗin kai, inda kuma aka karrama marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, wanda ya kira taron.
An yi wa taron take da: “National Unity Gathering for Prayers, Peace and Unity,” wanda ya samu halartar mambobin Isamic Movement of Nigeria da aka fi sani da Shi’ah, Ƙadiriyyah, Tijjaniyyah da Ahlus Sunnah tare da jagororin Kiristoci daga sassa daban-daban na faɗin Nijeriya. Mahalarta taron sun bayyana cewa, haɗuwar tana da nufin ƙarfafa haɗin kai a tsakanin ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari sa bambance-bambancen addini, aƙida ko ƙabila ba.
Da yake jawabi a taron Shugaban ƙungiyar CAN reshen Jihar Katsina, Reberen Richard Shuaibu Danliti, ya bayyana taron a,matsayin muhimmin matakin kira ga ci-gaban haɗin kan mabiya mabambanta addinai da haɗin kan ƙasa. Ya yaba wa waɗanda suka halarta duk da cewa an halaka wanda ya kira taron, yana ma cewa CAN za ta gina matsayarta kan sakamakonsa da cigaba daga inda aka tsaya kan ƙoƙarin tabbatar da haɗin kai a tsakanin ‘yan ƙasa a Nijeriya tare addu’ar fatan gudanar da zaɓukan 2027 lami lafiya.
Jagoran tafiyar Shi’ah a Nijeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya samu wakilcin Farfesa Abdullahi Yahaya, wanda ya ce za su cigaba da kira ga haɗin kan al’umma kamar yadda marigayin ya riƙa yin gabanin rasuwarsa.
