Kogi: ‘Yan bindiga sun sace shugaban makaranta da ɗalibai yayin da ake tsaka da rubuta NECO

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun ƙaddamar da farmaki a makarantar sakandare ta Opada-Olowa da ke Ƙaramar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi, inda suka yi awon-gaba da shugaban makaranta, jami’in sanya ido na jarrabawar NECO da ɗalibai guda huɗu.

Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya fara ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Talata yayin da ɗalibai ke tsaka da rubuta jarrabawa.

Mazauna yankin sun ce, wasu ‘yan bindiga cikin adadi mai yawa ne suka kutsa cikin garin, inda suka riƙa harbe-harbe domin tsorata su gabanin su kai farmaki a makarantar.

A cewarsu, sai da aka daina harbe-harben ne sannan suka gano cewa an farmaki makarantar. Waɗanda aka sacen sune Mista Nyada Deniel, Mista Solomon Audu da kuma ɗalibai huɗu.

Mazaunan sun ce an sace iya ɗalibai huɗu ne kaɗai saboda adadin waɗanda suka je makarantar a ranar ba su da yawa kasancewar jarrabawar da ake yi a lokacin ba kowa ke yin ta ba.

Maharan sun kuma kira makusantansa mutanen da suka yi garkuwa da su a yammacin Talatar inda suka ce musu suna buƙatar a ba su kuɗin kafin su sako su.

Baya ga haka ne aka baza jami’an soji, ‘yan sanda, ‘yan bijilante da mafarauta domin farauto masu garkuwar gami da ƙoƙarin ceto waɗanda al’amarin ya rutsa da su.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar ta bakin Kakakinta, ASP Saliu Oyiza Afusat ta ce, ta ƙaddamar da atisayen ceto mutanen bayan tabbatar da batun waɗanda aka sacen.

By Babaji

Leave a Reply