Sahun ƙarshe na ‘yan Nijeriya da aka kwaso daga Afirka ta Kudu ya iso Legas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jirigin ƙarshe da Gwamnatin Tarayya ta tura domin ɗebo ‘yan Nijeriya guda 308 daga ƙasar Afirka ta Kudu akan matsalolin hare-haren baƙi ya iso Legas, lamarin da ya kawo ƙarshen jigilar ‘yan ƙasa da suka maƙale a ƙasar.

Hakan na zuwa ne sakamakon yawan kai hare-hare akan ‘yan ƙasashen waje saboda ƙyamar baƙi da ‘yan ƙasar kudancin Afirkan ke nunawa a wasu sassa.

Rahotanni sun bayyana cewa, jirgin, wanda ya ɗebo wasu manyan jami’an gwamnati uku, ya isa filin jiragen sama na Murtala Muhammed ne da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar Laraba.

Wannan shi ne sahun ƙarshe na aikin ɗebowar yayin da gwamnatin tarayya ta jido ‘yan Nijeriya sama da guda 1,500 daga Afirka ta Kudu.

Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Bianca Odumegwu Ojukwu, ta yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa abin da ta kira da “jagoranci cikin hikima da ƙwarewa” ganin yadda aka dawo da ‘yan Nijeriyar cikin ƙoshin lafiya.

Haka kuma, ta yi maraba da dawowarsu da kuma bayyana farin cikinta akan haka, tana mai jinjina wa jami’an Afirka ta Kudu kan ƙoƙarinsu na ganin an yi nasara a atisayen ɗebowar.

By Babaji

Leave a Reply