Kofin Duniya: Sifaniya ta kai wasan ƙarshe bayan doke Faransa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙasar Sifaniya ta Nahiyar Turai ta yi nasarar tsallakewa zuwa zagayen wasan ƙarshe a gasar Kofin Duniya na 2026 bayan doke Faransa da ci 2 da 0.

‘Yan wasa Mikel Oyarzabal da Pedro Porro ne suka zura ƙwallayen da suka kori ‘yan koci Didier Deschamps a wasan na dab da na ƙarshe da aka gudanar a daren jiya Talata.

Wannan al’amari ya kawo ƙarshen fatan Les Bleus na lashe kofin da kuma rashin nasara a karon farko a gasar duk da cewa tana cikin ƙasashen da ke kan gaba da ake wa fatan lashe kofin.

Haka kuma, nasarar ta sa Sifaniya jin ƙamshin kofin a karo na biyu a tarihinta tun bayan da ta taɓa lashewa a shekarar 2010 da aka gudanar a ƙasar Afirka ta Kudu.

Gabanin wannan zango, ƙasar Faransa ta doke ƙasashen Sweden, Paraguay da Morokon su Achraf Hakimi da ƙoƙarin Kyaftin Kylian Mbappe.

Sifaniya a ɗaya gefen, ta kori Austria, Portugal ɗin su Cristiano Ronaldo da kuma Belgium yayin da aka zura mata mafi ƙarancin yawan ƙwallaye.

A yanzu, Sifaniya na dakon jiran ɗayan tawagar ƙasashe biyu na wasan da za a fafata a yammacin yau Laraba tsakanin Argentina da ta lashe kofin a 2022 da kuma Ingila.

By Babaji

Leave a Reply