Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE Gombe
Jam’iyyar APC ta bayyana Jamilu Ishiaku Gwamna a matsayin wanda ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar a jihar Gombe domin zaɓen shekarar 2027, bayan kammala zaben fidda gwani da aka gudanar a faɗin jihar.
Da yake sanar da sakamakon, shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na APC, Sanata Sani Abubakar Danladi, ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen ne cikin bin ƙa’idojin dokar zaɓe ta 2022 da kuma jagororin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC, tare da bin tsarin jam’iyya.
Ya ce jimillar masu kaɗa ƙuri’a da aka tantance sun kai 556,081 a dukkan ƙananan hukumomin jihar.
A cewarsa, sakamakon ƙarshe ya nuna cewa Jamilu Ishiaku Gwamna ya samu kuri’u 247,161 wanda ya ba shi nasarar zama zakara a zaɓen fidda gwani.
Ya bayyana cewa Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu kuri’u 12,120, yayin da Sa’idu Ahmed Alkali ya samu ƙuri’u 11,612.
“Ni, Sanata Sani Abubakar Danladi, ina sanar da cewa Jamilu Ishiaku Gwamna shi ne wanda ya yi nasara a wannan zaɓen fidda gwani, kuma shi ne halastaccen ɗan takarar gwamnan APC a zaɓen 2027,” in ji shi.
Danladi ya kuma bayyana cewa kwamitin ya karɓi wasiƙun janyewa daga wasu ‘yan takara biyu, Pantami da Alkali, amma bayan fara aikin zaɓe aka gabatar da su, inda har an riga an buga sunayensu a takardar kuri’a kuma an samu ƙuri’u a kansu.
Ya yaba wa shugabancin APC a matakin ƙasa da na jiha bisa goyon bayan da suka bayar wanda ya taimaka wajen gudanar da zaɓen cikin nasara.
Haka kuma ya jinjinawa ‘yan kwamitin zaɓen da jami’an tsaro bisa tabbatar da zaman lafiya da tsari yayin gudanar da aikin.
A ƙarshe, ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa samar da daidaito ga dukkan ‘yan takara da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da dimokuraɗiyya a jihar Gombe. Muhammadu Inuwa Yahaya
