Hajjin 2026: NAHCON ta kammala jigilar maniyyatan Nijeriya

Spread the love

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), ta yi nasarar kammala dakon maniyyatan Nijeriya zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin 2026 kafin wa’adin da aka tsara.

Wannan wani ɓangare ne na shirye-shiryen fara gudanar da ibadar ta bana da miliyoyin jama’ar Musulmi daga sassan duniya daban-daban suke halarta a ƙasa mai tsarki.

NAHCON ta sanar da cewa, jirgin ƙarshe na jigilar maniyyatan ya tashi ne da misalin ƙarfe 10:44 na safiyar Alhamis, 21 ga Mayun 2026, wanda shi ya kawo ƙarshen kammala aikin jigilar da aka fara tun ranar 3 ga Mayu.

A cewarta, an gudanar da jigilar jimillar jirage 98 cikin kwanaki 18, inda ake gudanar da kusan jirage biyar a kowace rana a tsawon aikin.

An bai wa Nijeriya kujerun maniyyata 50,000 domin Hajjin 2026, amma maniyyata 39,000 ne suka samu tafiya in aka ɗauke wakilan gwamnati da ma’aikatan NAHCON.

Haka kuma, ba a cike sauran kujerun ba saboda halin rashin lafiya da mutuwa da wasu suka yi bayan an riga an ba su biza.

Kazalika, hukumar ta yi godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa kammala aikin cikin lumana da nasara bisa haɗin kan dukkan masu ruwa da tsaki.

By Babaji