
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Ɗahiru Liman, da Mataimakin Shugaban Majalisar, Magaji Henry Danjuma, tare da shugabar Masu Rinjaye na Majalisar, Munira Suleiman Tanimu, sun zama ‘yan takarar Jamiyyar (APC) domin wakiltar mazaɓunsu bayan gudanar da tantancewar sulhu a sassa daban-daban na jihar.
An tabbatar da Hon. Dahiru Liman a matsayin ɗan takarar APC na mazaɓar Makera bayan an gudanar da zaɓen sulhu da ya samu halartar shugabannin jam’iyya, jami’an zaɓe da magoya baya.
Da yake bayyana sakamakon, jami’in tattara sakamakon zaɓen, Injiniya Ezekiel Samuel Gode, ya ce Liman ya zama ɗan takara ba tare da hamayya ba bayan amincewa da shi a matsayin ɗan takarar sulhu guda ɗaya na mazabar.
Ya ce, “Bayan karɓar sakamakon tabbatarwa daga rumfunan zaɓe guda biyar, kuma babu wani ɗan takara da ya tsaya takara tare da shi, ina ayyana Hon. Liman Tahiru a matsayin wanda aka tabbatar kuma aka dawo da shi a matsayin ɗan takarar APC na mazabar Makera.”
Hakazalika, Mataimakin Shugaban Majalisar, Hon. Barr. Magaji Henry Danjuma, ya samu tikitin APC na mazabar Kagarko bayan mambobin jam’iyyar daga gundumomi daban-daban sun tabbatar da takararsa ba tare da hamayya ba.
Jami’in zaɓen APC, Abdulrahman Ibrahim Apo Jere, ne ya sanar da nasarar Danjuma a cibiyar tattara sakamakon ƙaramar hukumar bayan kammala tsarin tabbatarwar.
Ita ma Shugabar Masu Rinjaye ta Majalisar, Hon. Munira Suleiman Tanimu, ta samu tikitin APC na mazabar Lere ta Gabas bayan an gudanar da zaɓen sulhu cikin lumana a gundumomi shida na mazabar.
Jami’in zaɓen mazabar Lere ta Gabas, Hon. Aminu Yaro, ya sanar da ita a matsayin ‘yar takarar jam’iyyar bayan kammala zaɓen da aka gudanar a Saminaka.
A wani mataki da ake ganin na ƙarfafa haɗin kan jam’iyya gabanin zaɓen shekarar 2027, wasu masu neman takarar kujerun Majalisar Dokokin Jihar Kaduna a ƙarƙashin APC sun janye daga takara tare da bayyana goyon bayansu ga ‘yan takarar sulhu na jam’iyyar.
Da yake jawabi a madadin waɗanda suka janye a Kaduna, Dakta Abdulrazaq Shuibu Labbo, mai neman takarar mazabar Kaka/Gogi ta Birnin Gwari, ya ce sun ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da shiga tsakani da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi domin tabbatar da haɗin kai a cikin jam’iyyar.
Ya ce, “Muna cikakken goyon baya ga shugabancin ci gaba na Gwamna Sanata Uba Sani, kuma muna sake tabbatar da aniyarmu ta ganin ya sake samun nasara tare da samun gagarumar nasarar APC a Jihar Kaduna da ma ƙasa baki ɗaya.”
Daga cikin waɗanda suka janye daga takara akwai Dr. Abdulrazaq Shuibu Labbo na Kaka/Gogi a Birnin Gwari, Mustapha Adam na Giwa ta Yamma, Deborah Musa ta Lere ta Yamma, Isah Nasidi na Doka/Gabasawa da Kabiru Bale Ahmed na Kawo.
Masu bibiyar harkokin siyasa sun bayyana cewa matakin na nuna yadda shugabancin APC a Kaduna ke ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kai tare da kauce wa rikice-rikicen cikin gida gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
