Yadda malami ɗaya ke koyar da yara fiye da 100 a Bauchi

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Fiye da yara 100 ne suke karatu a gindin bishiyoyi tun bayan iska ta rushe ginin azuzuwan makarantar Nomadic ta Kondawa da ke ƙaramar hukumar Jama’are a jihar Bauchi.

Shugaban Yakubu Ƴanmiɗi ya bayyanawa Blueprint Manhaja cewa tun bayan rugujewar makarantar shekaru shida da suka gabata, shi kaɗai yake yake koyar da ɗalibai sama da 100 a ƙarƙashin bishiyoyi.

Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al-umma (CITAD) a yau Alhamis, ta kai ɗauki makarantar ta hanyar rabon kayan karatu da kayan makaranta tare da samar da ƙarin malamai uku, yayin da masu ruwa da tsaki ke kira ga gwamnati da ta gaggauta sake gina makarantar domin ceto makomar yaran yankin.

Malam Isa Garba shi ne babban jami’in shirye-shirye na CITAD ya bayyana cewa tunda damina ta yaye makarantar shekara shida kuma akwai ɗalibai a yankin inda ya ce haka ne ya sa CITAD ta garzayo domin tallafawa.

Ya ƙara da cewa ” Waɗannan yara suna buƙatar a nusar da su ne domin hankalin su ya je zuwa ga karatu hakan ya sa mu ka zo muka raba masu kayan makaranta da littattafai rubutu tare da ɗaukar malamai guda uku domin su taimakawa Malami ɗaya tilo.

Mun yi wannan ne domin ya zama zabuwarwa ga ɗaliban da iyayensu mu ku ka hankalin hukumar ilimi ta jihar Bauchi wajen ganin cewa ta leƙo ta bada tagomashi da su kansu iyayen gida domin tabbatar da cewa yaran nan sun sami ilimi” in ji Isa Garba

A daidai lokacin da damina ta kankama, al’ummar yankin suna nuna damuwa kan yadda yara ke ci gaba da karatu ba tare da azuzuwa ba, lamarin da ke haddasa tsaikon karatu a duk lokacin da aka yi ruwan sama.

By ukarofi