Rikicin da ke ci gaba tsakanin Hukumar Kula da Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kaya ta ƙasa (FCCPC) da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ya jefa kasuwar bashin katin kira da intanet wadda ke da darajar kusan Naira biliyan 400 cikin ruɗani, tare da haddasa cikas ga miliyoyin masu amfani da sadarwa a faɗin ƙsar.
Saboda wannan saɓani na doka da iko tsakanin hukumomin biyu, wasu manyan kamfanonin sadarwa sun dakatar da tsarin bayar da rancen katin kira ga abokan hulɗarsu na ɗan lokaci. Wannan mataki ya jefa miliyoyin ‘yan Nijeriya cikin wahala, musamman masu ƙaramin ƙarfi da suka dogara da wannan tsari wajen ci gaba da amfani da waya.
Tsarin rancen katin kira, wanda kamfanonin sadarwa suka ƙirƙira domin sauƙaƙa wa masu amfani da ke ƙasan matakin samun kuɗin shiga, ya zama wata muhimmiyar hanyar rayuwa ga ’yan kasuwa, masu sana’o’i da sauran marasa kuɗi. Ta wannan tsari, kwastamomi kan karɓi katin kira ko data su biya a lokacin da suka sake saka kati.
Sai dai rikicin tsakanin FCCPC da NCC ya jefa wannan tsarin cikin barazana, duk da cewa Kotun Tarayya ta taɓa yanke hukunci kan batun. Abin takaici, rahotanni sun nuna cewa hukumomin biyu ba su bi wannan umarnin kotu yadda ya kamata ba, lamarin da ya ƙara dagula al’amura.
Shugaban ƙungiyar Masu Samar da Sadarwa ta Nijeriya (ALTON), Gbenga Adebayo, ya bayyana cewa tsarin rancen katin ya zama wata muhimmiyar hanyar rayuwa ga masu ƙaramin ƙarfi, inda ya cike giɓi a cikin al’umma da kusan kashi 60 cikin ɗari, waɗanda ba su da damar amfani da tsarin banki na yau da kullum.
Ya ce, wannan rikici ba kawai matsalar gudanarwa ba ce tsakanin hukumomi biyu, amma barazana ce ga tsarin tattalin arzikin sadarwa da kuma amincin masu zuba jari.
A cewarsa, “Abin da ke faruwa a kasuwar katin kira ba kawai rikici ba ne tsakanin hukumomi, gwaji ne kan yadda tsarin da ke gina amincewar kasuwanci a ƙasar nan ke aiki ko kuma gazawa.”
ALTON ta kuma nuna damuwa cewa duk da akwai umarnin kotu, har yanzu ana ci gaba da rashin bin doka, abin da ke ƙara dagula amincewar masu zuba jari da kuma jawo ruɗani a masana’antar sadarwa.
Masu ruwa da tsaki a fannin sun yi gargaɗin cewa ci gaba da wannan rikici na iya rage kwarin gwiwar masu zuba jari na ƙasashen waje, musamman a fannin tattalin arzikin zamani wanda ke buƙatar tsayayyen tsari na doka da gudanarwa.
Rahotanni sun nuna cewa Nijeriya ta samu sama da dala biliyan 100 na zuba jari a fannin sadarwa cikin shekaru 25 da suka gabata, wanda ya haifar da gagarumin bunƙasa daga layukan waya 600,000 a shekarar 2001 zuwa sama da layi miliyan 220 a yau.
Wannan ci gaba ya nuna yadda ɓangaren sadarwa ya zama zaya daga cikin ginshiƙan tattalin arzikin ƙasa, har ya zarce tsarin banki a yaɗuwa, inda har yanzu wasu ƙananan hukumomi ba su da bankuna amma suna da layukan sadarwa.
Jaridar Blueprint ta bayyana damuwarta cewa wannan rikici da za a iya kauce masa tsakanin FCCPC da NCC na iya jawo koma-baya ga kwararar zuba jari zuwa Nijeriya.
Baya ga barazanar tattalin arziki, dakatar da tsarin rancen kati na haifar da wahala ga miliyoyin ‘yan Nijeriya da ke dogaro da shi wajen gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.
A ƙarshe, muna tare da kiran ƙungiyar ALTON wajen roƙon FCCPC da NCC su mutunta umarnin Kotun Tarayya, su kuma gaggauta warware wannan rikici cikin tsari. Haka kuma, ya dace Gwamnatin Tarayya ta sa baki domin dawo da zaman lafiya a tsakanin hukumomin biyu, tare da kare tattalin arzikin ƙasa da jin daɗin ’yan ƙasa.
